Ka faɗa masa, ni Ubangiji Allah na ce, Ga shi, ina gāba da shi, wato Dutsen Seyir. Zan miƙa hannuna gāba da shi, Zan maishe shi kufai, in lalatar da shi.
don haka, ni Ubangiji na ce, hakika zan sa a zub da jininsa. Mai zub da jini zai fafare shi, da yake shi ma ya zub da jini, domin haka mai zub da jini zai fafare shi.
domin haka, ni Ubangiji Allah na ce, hakika zan saka masa gwargwadon fushinsa, da kishinsa, da ƙiyayyar da ya nuna musu. Zan sanar da kaina a gare su sa'ad da na hukunta shi.
Kamar yadda ya yi farin ciki saboda gādon jama'ar Isra'ila, da ya zama kufai marar amfani, haka nan zan yi da shi, wato Seyir. Zai zama kufai marar amfani, wato Dutsen Seyir da dukan Edom. Sa'an nan mutane za su sani ni ne Ubangiji!”