“Ku ji wannan, ya ku firistoci! Ku saurara, ya mutanen Isra'ila! Ku kasa kunne, ya gidan sarki! Gama za a yi muku hukunci, Domin kun zama tarko a Mizfa, Da ragar da aka shimfiɗa a bisa Tabor.
Girmankan mutanen Isra'ila yana ba da shaida a kansu. Mutanen Ifraimu za su yi tuntuɓe cikin laifinsu. Mutanen Yahuza kuma za su yi tuntuɓe tare da su.
“Sa'ad da Ifraimu ta ga ciwonta, Yahuza kuma ta ga rauninta, Sai Ifraimu ta aika zuwa Assuriya, Wurin babban sarki. Amman ba zai iya warkar da ciwonki, ko rauninki ba.