Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona, Da ku da kuke tsammani kuna zaman lafiya a Samariya, Ku da kuke manyan mutane Na wannan babbar al'umma ta Isra'ila, Waɗanda jama'a suke zuwa a gare su neman taimako!
Ku je ku duba a birnin Kalne. Sa'an nan ku zarce zuwa babban birnin Hamat, Har zuwa birnin Gat ta Filistiyawa. Sun fi mulkin Yahuza da Isra'ila ne? Ko kuwa, yankin ƙasarsu ya fi naku?
Ubangiji kansa ne ya rantse. Ubangiji Allah Mai Runduna ya ce, “Ba na son girmankai na jama'ar Isra'ila. Ba na son fādodinsu. Zan ba da birnin da dukan abin da yake cikinsa ga abokan gābansu.”
Sa'ad da dangin mamacin ya shiga don ya fitar da gawar, ya ƙone, sai ya yi kira ga ko wane ne da yake ɓoye a gidan, ya ce, “Ko akwai wani kuma a nan?” Sai a amsa, “A'a.” Zai ce, “Kul! Kada a ambaci sunan Ubangiji.”
Ubangiji Allah Mai Runduna kansa, ya amsa ya ce, “Zan aiko da wata al'umma ta yi gāba da ku, ya Isra'ilawa. Za ta matse muku Tun daga mashigin Hamat wajen arewa, Har zuwa Kwarin Urdun a kudu.”