Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Sai Yunusa ya yi addu'a ga Ubangiji Allah a cikin cikin kifin, |
| 2 |
| ya ce, “A cikin wahalata na yi kira gare ka, ya Ubangiji, Ka a kuwa amsa mini. Daga can cikin lahira na yi kira, Ka kuwa ji muryata. |
| 3 |
| Ka jefa ni cikin zurfi, Can cikin tsakiyar teku, Inda igiyoyin ruwa suka kewaye ni, Kumfa da raƙuman ruwanka suka bi ta kaina. |
| 4 |
| Na ce, an kore ni daga wurinka, Duk da haka zan sāke ganin Haikalinka mai tsarki. |
| 5 |
| Ruwa ya sha kaina, Tekun ta rufe ni ɗungum. Tsire-tsiren teku suka naɗe kaina. |
| 6 |
| Na tafi can ƙasa ƙarƙashin tussan duwatsu. Ƙasar da ƙofarta take rufe har abada, Amma ka fitar da ni daga cikin ramin, ya Ubangiji Allahna. |
| 7 |
| Sa'ad da na ji raina yana rabuwa da ni, Sai na tuna da kai, ya Ubangiji. Addu'ata kuwa ta kai gare ka a Haikalinka tsattsarka. |
| 8 |
| Su waɗanda suke yin sujada ga gumaka marasa amfani Sun daina yi maka biyayya. |
| 9 |
| Amma ni zan raira yabbai gare ka, Zan miƙa maka sadaka, Zan cika wa'adin da na yi. Ceto daga wurin Ubangiji yake.” |
| 10 |
| Ubangiji kuwa ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunusa a gaɓar teku. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/jonah/002.mp3
4
2