Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Daga ciki cikin kifi, Yunana ya yi addu’a ga Ubangiji Allahnsa. |
| 2 |
| Ya ce, “A cikin damuwata na yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini. Daga cikin zurfi kabari na yi kiran neman taimako, ka kuwa saurari kukata. |
| 3 |
| Cikin tashin hankali, ka jefa ni cikin zurfafa, a tsakiyar teku, ka kuma jujjuya ni a cikin ruwa; dukan raƙuman ruwanka da ambaliyarka sun bi ta kaina. |
| 4 |
| Sai na ce, ‘An kore ni daga fuskarka; duk da haka zan sāke duba wajen haikalinka mai tsarki.’ |
| 5 |
| Ruwayen da suke kewaye da ni sun yi mini barazana, zurfi kuma ya kewaye ni, ciyayin ruwa suna nannaɗe kewaye da ni. |
| 6 |
| Na nutsa har ƙarƙashin tuddai; a ƙarƙashin duniya, ka rufe ni har abada. Amma ka dawo da raina daga rami, Ya Ubangiji Allahna. |
| 7 |
| “Sa’ad da na ji raina yana rabuwa da ni, na tuna da kai ya Ubangiji, addu’ata kuma ta kai gare ka, a haikalinka mai tsarki. |
| 8 |
| “Waɗanda suka maƙale wa gumaka marasa amfani, sukan ƙyale alherin da zai kasance nasu. |
| 9 |
| Amma ni, da waƙar godiya, zan miƙa tawa hadaya gare ka. Abin da na yi alkawari, shi ne zan yi. Ceto yakan zo ne kawai daga wurin Ubangiji.” |
| 10 |
| Sai Ubangiji ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunana a gaɓan teku. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/jonah/002.mp3
4
2