Sojojin dawakai suna kai sura, Takuba suna walƙiya, māsu suna ƙyalƙyali. Ga ɗumbun kisassu, da tsibin gawawwaki, Matattu ba su ƙidayuwa, Suna tuntuɓe a kan gawawwaki!
Ya faru saboda yawan karuwancin Nineba kyakkyawa mai daɗin baki, Wadda ta ɓad da al'umman duniya da karuwancinta, Ta kuma ɓad da mutane da daɗin bakinta.
Duk da haka an tafi da ita, an kai ta cikin bauta. An fyaɗa ƙanananta a ƙasa, An yi kacakaca da su a kowace mararraba. An jefa kuri'a a kan manyan mutanenta, Aka ɗaure dukan manyan mutanenta da sarƙoƙi.
Shugabanninki kamar ɗango suke, Manyan mutanenki kamar cincirindon fāra ne, Suna zaune a kan shinge a kwanakin sanyi, Sa'ad da rana ta fito, sukan tashi su tafi, Ba wanda ya san inda suke.