Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Da na ɗaga idona, sai ga wani mutum yana riƙe da igiyar awo. |
| 2 |
| Sai na ce, “Ina za ka?” Ya ce mini, “Zan tafi in auna Urushalima don in san fāɗinta da tsawonta.” |
| 3 |
| Sai ga mala'ikan da yake magana da ni, ya fita, sai wani mala'ika kuma ya zo ya sadu da shi. |
| 4 |
| Ya ce masa, “Ka yi gudu, ka faɗa wa saurayin can, cewa za a zauna a Urushalima kamar a ƙauyuka marasa garu, saboda yawan mutane da dabbobi da suke cikinta. |
| 5 |
| Gama zan zama mata garu na wuta kewaye da ita, zan zama daraja a tsakiyarta, in ji Ubangiji.” |
| 6 |
| Ubangiji ya ce, “Yanzu ku gudu daga ƙasar arewa, gama na warwatsa ku a waje kamar iska ta kusurwoyi huɗu na duniya! |
| 7 |
| Ya ke Sihiyona, ku tsere, ku waɗanda kuke zaune a Babila.” |
| 8 |
| Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Bayan ɗaukaka ya aike ni zuwa wurin al'umman duniyan nan da suka washe ku, gama wanda ya taɓe ku, ya taɓi ƙwayar idona. |
| 9 |
| Ga shi, zan nuna ikona a kansu, za su kuwa zama abin waso ga waɗanda suka bauta musu. Sa'an nan za ku sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni. |
| 10 |
| “Ki raira waƙa, ki yi farin ciki, ya Sihiyona, gama ina zuwa, in zauna a tsakiyarki! Ni Ubangiji na faɗa. |
| 11 |
| “A wannan rana al'umman duniya da yawa za su haɗa kai da Ubangiji, za su kuwa zama jama'ata, ni kuma zan zauna a tsakiyarki. Za ki sani Ubangiji Mai Runduna ya aike ni gare ki. |
| 12 |
| Yahuza za ta zama abin mallakar Ubangiji a cikin tsattsarkar ƙasar. Zai kuma zaɓi Urushalima.” |
| 13 |
| Bari dukan 'yan adam su yi tsit a gaban Ubangiji, gama ya taso daga wurin zamansa mai tsarki. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/zechariah/002.mp3
14
2