Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Da na ɗaga idona sama kuma, sai na ga littafi mai tashi a sama. |
| 2 |
| Sai mala'ikan ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?” Na amsa, “Na ga littafi mai tashi a sama, tsawonsa kamu ashirin ne, fāɗinsa kuma kamu goma.” |
| 3 |
| Sa'an nan ya ce mini, “Wannan la'ana ce wadda take tashi bisa ƙasa duka. Gama za ta datse ɓarawo da mai rantsuwa da ƙarya. |
| 4 |
| Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Zan aika da littafin a gidan ɓarawo da gidan mai rantsuwa da sunana a kan ƙarya. Littafin zai zauna a gidansa, ya ƙone gidan, da katakan, da duwatsun.’ ” |
| 5 |
| Sa'an nan mala'ikan da yake magana da ni ya matso, ya ce mini, “Ka ɗaga idonka, ka ga abin nan da yake fitowa.” |
| 6 |
| Ni kuwa na ce masa, “Mene ne wannan?” Ya ce, “Wannan babban kwando ne wanda ya fita.” Ya kuma ce, “Wannan mugunta ce a dukan ƙasar.” |
| 7 |
| Da aka ɗaga murfin kwando na darma, sai ga mace tana zaune a cikin kwandon! |
| 8 |
| Sai ya ce, “Wannan mugunta ce.” Sa'an nan ya tura ta cikin kwandon, ya rufe bakin kwandon da murfi na darma mai nauyi. |
| 9 |
| Da na ɗaga idona, sai na ga mata biyu suna matsowa. Iska tana hura fikafikansu, gama suna da fikafikai kamar na shamuwa. Suka ɗaga kwandon sama. |
| 10 |
| Sai na tambayi mala'ikan da yake magana da ni, na ce, “Ina za su kai kwandon?” |
| 11 |
| Ya ce mini, “Za su tafi da shi ƙasar Shinar don su gina masa haikali, sa'ad da suka gama ginin, za su ajiye shi a ciki.” |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/zechariah/005.mp3
14
5