Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Na sāke dubawa sai ga naɗaɗɗen littafi mai firiya a gabana! |
| 2 |
| Sai ya tambaye ni ya ce, “Me ka gani?” Sai na amsa na ce, “Na ga naɗaɗɗen littafi mai firiya, tsawonsa ƙafa talatin da fāɗinsa kuma ƙafa goma sha biyar.” |
| 3 |
| Sai ya ce mini, “Wannan ce la’anar da za tă ratsa dukan ƙasar; gama bisa ga abin da ya ce a gefe ɗaya, za a kawar da kowane ɓarawo, kuma bisa ga abin da ya ce a ɗaya gefen za a kawar da duk mai rantsuwar ƙarya. |
| 4 |
| Ubangiji Maɗaukaki ya ce, ‘Zan aika shi, zai shiga gidan ɓarawo, da gidan mai rantsuwar ƙarya da sunana. Zai kasance a gidansa yă hallaka gidan da katakon da duwatsun.’ ” |
| 5 |
| Sai mala’ikan da yake mini magana ya zo gaba ya ce mini, “Duba ka gani ko mene ne wannan da yake fitowa.” |
| 6 |
| Na tambaya na ce, “Mene ne?” Ya amsa ya ce, “Kwando ne na awo.” Ya ƙara da cewa, “Wannan shi ne laifin mutanen a duk fāɗin ƙasar.” |
| 7 |
| Sa’an nan aka ɗaga murfin dalman, a ciki kuwa ga mace zaune! |
| 8 |
| Ya ce, “Wannan mugunta ce,” ya kuma tura ta cikin kwandon ya rufe da murfin dalman, ya kuma danna da dutse. |
| 9 |
| Na ɗaga idona sama, sai ga mata biyu a gabana, iska tana hura fikafikansu! Suna da fikafikai kamar na shamuwa, suka kuma ɗaga kwandon sama. |
| 10 |
| Na tambayi mala’ikan da yake magana da ni na ce, “Ina za ku kai kwandon?” |
| 11 |
| Ya amsa ya ce, “Zuwa ƙasar Babiloniya don a gina masa haikali. Sa’ad da aka gama ginin, za a ajiye shi a ciki.” |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/zechariah/005.mp3
14
5