Sabon Rai Don Kowa 2020
|
| 1 |
| Ubangiji ya ce wa Musa, |
| 2 |
| “Ka yi magana da Isra’ilawa, ka kuma karɓi sanduna goma sha biyu daga wurinsu, sanda guda daga kowane shugaban gidan kakanninsu. Ka rubuta sunan kowa a sandansa. |
| 3 |
| A kan sandan Lawi kuwa ka rubuta sunan Haruna, gama dole a sami sanda ɗaya saboda shugaban gidan kakanninsu. |
| 4 |
| Ka ajiye su a Tentin Sujada, a gaba akwatin Alkawari, inda zan sadu da kai. |
| 5 |
| Sandan mutumin da na zaɓa zai yi toho, da haka zan raba kaina da gunagunin da Isra’ilawa suke yi.” |
| 6 |
| Saboda haka Musa ya yi magana da Isra’ilawa, sai shugabanninsu suka ba shi sanduna goma sha biyu, sanda ɗaya don shugaba, bisa ga gidajen kakanninsu, sandan Haruna kuma yana a cikinsu. |
| 7 |
| Sai Musa ya ajiye sandunan a gaban Ubangiji a cikin Tentin Sujada. |
| 8 |
| Kashegari da Musa ya shiga cikin Tentin Sujada sai ga sandan Haruna na gidan Lawiyawa ya yi toho, ya yi furanni, ya kuma yi ’ya’yan almon. |
| 9 |
| Sai Musa ya fitar wa dukan Isra’ilawa dukan sandunan da suke daga gaban Ubangiji. Suka duba, kowa kuma ya ɗauki sandansa. |
| 10 |
| Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka mayar da sandan Haruna a akwatin Alkawari, don a ajiye shi alama ga masu tawaye. Wannan zai kawo ƙarshen gunaguninsu a kaina, domin kada su mutu.” |
| 11 |
| Musa kuwa ya aikata kamar dai yadda Ubangiji ya umarce shi. |
| 12 |
| Sai Isra’ilawa suka ce wa Musa, “To, ai in haka ne, mun ƙare ke nan! |
| 13 |
| Idan an ce duk wanda ya zo kusa da tabanakul na Ubangiji zai mutu, ai rayuwarmu kamar mun mutu ke nan.” |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/numbers/017.mp3
36
17