Hakika ina gaya muku, a cikin duk waɗanda mata suka haifa, ba wanda ya bayyana da ya fi Yahaya Maibaftisma girma. Duk da haka, wanda ya fi ƙanƙanta a Mulkin Sama ya fi shi.
Ga Ɗan Mutum ya zo, yana ci yana sha, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama, mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi!’ Duk da haka hikimar Allah, ta aikinta ne ake tabbatar da gaskiyarta.”
“Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, suna sanye da tsumma, suna hurwa da toka.
Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi, har Hades. Da mu'ujizan da aka yi a cikinki, su aka yi a Saduma, da ta wanzu har ya zuwa yau.
A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin Sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai.