|
| 1 |
|
| Sai ya sāke shiga majami'a. Akwai wani mutum a nan kuwa mai shanyayyen hannu. |
|
| 2 |
|
| Sai suka yi haƙwansa su ga ko zai warkar da shi ran Asabar, don su samu su kai ƙararsa. |
|
| 3 |
|
| Sai ya ce wa mai shanyayyen hannun, “Fito nan fili.” |
|
| 4 |
|
| Ya ce musu, “Ya halatta ran Asabar a yi alheri ko kuwa mugunta? A ceci rai, ko kuwa a kashe shi?” Amma sai suka yi shiru. |
|
| 5 |
|
| Da ya duddube su da fushi, yana baƙin ciki da taurin zuciyarsu, sai ya ce wa mutumin, “Miƙo hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye. |
|
| 6 |
|
| Da Farisiyawa suka fita, nan da nan suka yi shawara da mutanen Hirudus a kansa, yadda za su hallaka shi. |
|
| 7 |
|
| Sai Yesu ya tashi tare da almajiransa, suka je bakin tekun. Taro mai yawan gaske kuwa daga ƙasar Galili ya biyo shi, har ma daga ƙasar Yahudiya, |
|
| 8 |
|
| da Urushalima, da ƙasar Edom, da hayin Kogin Urdun, da kuma wajen Taya da Sidon, babban taro ya zo wurinsa, don sun ji labarin duk abin da yake yi. |
|
| 9 |
|
| Don gudun kada taron ya mammatse shi kuwa, sai ya ce wa almajiransa su keɓe masa ƙaramin jirgi guda, |
|
| 10 |
|
| saboda ya riga ya warkar da mutane da yawa, har ya kai ga duk masu cuta na dannowa wurinsa domin su taɓa shi. |
|
| 11 |
|
| Baƙaƙen aljannu kuwa, duk sa'ad da suka gan shi, sai su fāɗi gabansa suna kururuwa, suna cewa, “Kai Ɗan Allah ne.” |
|
| 12 |
|
| Sai ya kwaɓe su ƙwarai kada su bayyana shi. |
|
| 13 |
|
| Ya hau dutse, ya kira waɗanda yake so, suka je wurinsa. |
|
| 14 |
|
| Ya zaɓi mutum goma sha biyu su zauna tare da shi, ya riƙa aikensu suna wa'azi. |
|
| 15 |
|
| Ya kuma ba su ikon fitar da aljannu. |
|
| 16 |
|
| Ga waɗanda ya zaɓa, Bitrus, |
|
| 17 |
|
| da Yakubu ɗan Zabadi, da kuma ɗan'uwansa Yahaya, ya sa musu suna Buwanarjis, wato 'ya'yan tsawa. |
|
| 18 |
|
| Sai kuma Andarawas, da Filibus, da Bartalamawas, da Matiyu, da Toma, da Yakubu ɗan Halfa, da Yahuza, da Saminu Bakan'ane, |
|
| 19 |
|
| da kuma Yahuza Iskariyoti wanda ya bāshe shi. Sa'an nan ya shiga wani gida. |
|
| 20 |
|
| Taron kuwa ya sāke haɗuwa har ya hana su cin abinci. |
|
| 21 |
|
| Da 'yan'uwansa suka ji haka, sai suka fita su kamo shi, saboda sun ce, “Ai, ya ruɗe.” |
|
| 22 |
|
| Malaman Attaura kuwa da suka zo daga Urushalima sai suka ce, “Ai, Ba'alzabul ne ya hau shi, da ikon sarkin aljannu kuma yake fitar da aljannu.” |
|
| 23 |
|
| Sai Yesu ya kira su, ya ba su misali da cewa, “Ina Shaiɗan zai iya fitar da Shaiɗan? |
|
| 24 |
|
| Ai, in mulki ya rabu a kan gāba, wannan mulki ba zai ɗore ba. |
|
| 25 |
|
| Haka in gida ya rabu a kan gāba, wannan gida ba zai ɗore ba. |
|
| 26 |
|
| Shaiɗan kuma in ya tayar wa kansa, ya rabu, ba zai ɗore ba, ƙarewa tasa ce ta zo. |
|
| 27 |
|
| Ba mai iya shiga gidan ƙaƙƙarfan mutum ya washe kayansa, sai ko ya fara ɗaure ƙaƙƙarfan mutumin, sa'an nan kuma ya washe gidansa. |
|
| 28 |
|
| “Hakika, ina gaya muku, ā gafarta wa 'yan adam duk zunubansu, da kowane saɓon da suka hurta, |
|
| 29 |
|
| amma fa, duk wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki ba ya samun gafara har abada, ya yi madawwamin zunubi ke nan.” |
|
| 30 |
|
| Wannan kuwa don sun ce, “Yana da baƙin aljan ne.” |
|
| 31 |
|
| Sa'an nan uwa tasa da 'yan'uwansa suka zo. Suna tsaye a waje, sai suka aika masa yă je. |
|
| 32 |
|
| Taro kuwa na zaune kewaye da shi, sai suka ce masa, “Ga tsohuwarka da 'yan'uwanka suna nemanka a waje.” |
|
| 33 |
|
| Ya amsa musu ya ce, “Su wane ne tsohuwata da 'yan'uwana?” |
|
| 34 |
|
| Sai ya waiwayi waɗanda suke zaune kewaye da shi, ya ce, “Ga tsohuwata a nan da 'yan'uwana! |
|
| 35 |
|
| Ai, kowa ya yi abin da Allah yake so, shi ne ɗan'uwana, ita ce 'yar'uwata, ita ce kuma tsohuwata.” |
|
|
|
|