Bayan kwana biyar sai babban firist, Hananiya, ya zo tare da waɗansu shugabanni, da kuma wani lauya, mai suna Tartulus, suka yi ƙarar Bulus a gaban mai mulki.
Da aka kirawo Tartulus, ya shiga kai ƙarar Bulus, ya ce, “Ya mafifici Filikus, tun da yake ta gare ka ne muke zaman lafiya ƙwarai, ta tsinkayarka ne kuma ake kyautata zaman jama'armu,
Da mai mulki ya alamta wa Bulus ya yi magana, sai ya amsa ya ce, “Tun da na sani ka yi shekaru da yawa kana yi wa jama'ar nan shari'a, da farin ciki zan kawo hanzarina.
Amma na yarda cewa, bisa ga hanyar nan da suke kira ‘Ɗariƙa’ nake bauta wa Allahn kakanninmu, nake kuma gaskata duk abin da yake a rubuce a cikin Attaura da kuma littattafan annabawa.
sai ko maganar nan ɗaya tak, da na ɗaga murya na faɗa, sa'ad da nake a tsaye a cikinsu, cewa, ‘Game da maganar tashin matattu ake yi mini shari'a a gabanku yau.’ ”
Bayan 'yan kwanaki Filikus ya zo tare da matarsa, Durusila, wata Bayahudiya. Sai ya aika a zo da Bulus, ya kuwa saurare shi a kan maganar gaskatawa da Almasihu Yesu.
Bulus yana ba da bayani a kan adalci, da kamunkai, da kuma hukuncin nan mai zuwa, Filikus ya kaɗu, ya kāda baki ya ce, “Yanzu kam, sai ka koma. In na sami zarafi nā kira ka.”