Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| A zamanin dā, Allah ya yi wa kakannin kakanninmu magana ta hanyoyi masu yawa iri iri, ta bakin annabawa, |
| 2 |
| amma a zamanin nan na ƙarshe, sai ya yi mana magana ta wurin Ɗansa, wanda ya sa magājin kome, wanda ta wurinsa ne kuma ya halicci duniya. |
| 3 |
| Shi ne hasken ɗaukakar Allah, ainihin kamannin zatinsa kuma, shi kuma yana a riƙe da dukan abubuwa ta ikon faɗarsa. Bayan da ya tsarkake zunubanmu, sai ya zauna a dama da Maɗaukaki a can Sama. |
| 4 |
| Ta haka yake da fifiko a kan mala'iku, kamar yadda sunansa da ya gāda yake da fifiko nesa a kan nasu. |
| 5 |
| Domin kuwa wane ne a cikin mala'iku Allah ya taɓa ce wa, “Kai Ɗana ne, Ni Ubanka ne yau”? da kuma, “Zan kasance Uba a gare shi, Shi kuma, zai kasance Ɗa a gare ni”? |
| 6 |
| Amma da zai sāke shigo da magāji a duniya, sai ya ce, “Dukkan mala'ikun Allah su yi masa sujada.” |
| 7 |
| A game da mala'iku kuma sai ya ce, “Yakan mai da mala'ikunsa ruhohi, Masu hidimarsa kuma harsunan wuta.” |
| 8 |
| Amma a game da ɗan, sai ya ce, “Kursiyinka, ya Allah, na har abada abadin ne, Sandar sarautarka sanda ce ta tsantsar gaskiya. |
| 9 |
| Kā ƙaunaci aikin adalci, kā ƙi aikin sāɓo. Saboda haka Allah, wato, Allahnka, ya shafe ka Da man farin ciki fiye da tsararrakinka.” |
| 10 |
| Da kuma, “Ya ubangiji, kai ne ka halicci duniya tun farko, Sammai kuma aikinka ne. |
| 11 |
| Su za su hallaka, amma kai madawwami ne. Duk za su tsufa kamar tufa, |
| 12 |
| Za ka naɗe su kamar mayafi, Za su kuma sauya, Amma kai kana nan ba sākewa, Har abada shekarunka ba za su ƙare ba.” |
| 13 |
| Amma wane ne a cikin mala'iku Allah ya taɓa ce wa, “Zauna a damana, Sai na sa ka take maƙiyanka”? |
| 14 |
| Ashe, dukan mala'iku ba ruhohi masu hidima ba ne, waɗanda Allah yakan aika, don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima? |
|
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/hebrews/001.mp3
13
1