Littafi Mai Tsarki 1979
|
| 1 |
| Rabon zuriyar Yusufu ya milla tun daga Urdun zuwa wajen Yariko, gabas da ruwan Yariko zuwa jejin. Ya haura daga Yariko zuwa ƙasar tuddai zuwa Betel. |
| 2 |
| Daga Betel ya miƙa zuwa Luz, sa'an nan ya zarce zuwa Atarot, karkarar Arkiyawa. |
| 3 |
| Sai ya gangara yamma zuwa karkarar Yafletiyawa har zuwa karkarar Bet-horon wadda take cikin kwari. Ya zarce kuma zuwa Gezer, sa'an nan ya gangara a teku. |
| 4 |
| A nan ne jama'ar Yusufu, wato Manassa da Ifraimu, suka sami nasu gādo. |
| 5 |
| Karkarar jama'ar Ifraimu, bisa ga iyalansu, ita ce iyakar gādonsu a wajen gabas, wato ita ce Atarot-addar har zuwa Bet-horon wadda take kan tudu. |
| 6 |
| Daga can iyakar ta miƙa zuwa teku ta bar Mikmetat a wajen arewa. A wajen gabas kuwa iyakar ta karkata zuwa Ta'anat-Shilo, daga can sai ta zarce gaba a wajen gabas zuwa Yanowa. |
| 7 |
| Daga Yanowa sai ta gangara zuwa Atarot da Nayaran, ta kuma gegi Yariko, sa'an nan ta gangara a Urdun. |
| 8 |
| Daga Taffuwa, sai iyakar ta yi yamma zuwa rafin Kana, sa'an nan ta gangara a teku. Wannan shi ne gādon Ifraimawa bisa ga iyalansu, |
| 9 |
| tare da garuruwan da ƙauyukan da aka keɓe wa Ifraimawa daga cikin gādon jama'ar Manassa. |
| 10 |
| Amma ba su kori Kan'aniyawa da suke zaune a Gezer ba, don haka Kan'aniyawa ka zauna tare da Ifraimawa har wa yau, amma Kan'aniyawa suka zama bayi masu yin aikin dole. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/joshua/016.mp3
24
16