|
| 1 |
| Daga dattijon nan na ikkilisiya zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya, da 'ya'yanta waɗanda nake ƙauna da gaske, ba kuwa ni kaɗai ba, har ma dukan waɗanda suka san gaskiya, |
| 2 |
| wato, muna ƙaunarku saboda gaskiyar da take a dawwame a cikinmu, za ta kuwa kasance tare da mu har abada. |
| 3 |
| Alheri, da jinƙai, da salama na Allah Uban, da kuma na Yesu Almasihu Ɗan Uban, za su tabbata a gare mu, da gaskiya da ƙauna. |
| 4 |
| Na yi farin ciki ƙwarai da samun waɗansu 'ya'yanki suna bin gaskiya, kamar yadda Uba ya ba mu umarni. |
| 5 |
| Yanzu kuma ina roƙonki, uwargida, ba cewa wani sabon umarni nake rubuto miki ba, sai dai wanda muke da shi tun farko ne, cewa mu ƙaunaci juna. |
| 6 |
| Ƙauna kuwa ita ce mu bi umarninsa. Umarnin kuwa, shi ne kamar yadda kuka ji tun farko, cewa ku yi zaman ƙauna. |
| 7 |
| Gama masu ruɗi da yawa sun fito duniya, waɗanda ba sa bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana da jiki, irin wannan shi ne mai ruɗi, magabcin Almasihu. |
| 8 |
| Ku kula da kanku don kada ku yar da aikin da muka yi, amma dai ku sami cikakken sakamako. |
| 9 |
| Kowa ya yi ƙari, bai tsaya a kan koyarwar Almasihu ba, Allah ba ya tare da shi ke nan. Wanda kuwa ya tsaya a kan koyarwar nan, yana da uba da Ɗan. |
| 10 |
| Kowa ya zo gare ku, bai kuwa zo da wannan koyarwa ba, kada ku karɓe shi a gidanku, ko maraba ma kada ku yi masa. |
| 11 |
| Don duk wanda ya yi masa maraba, mugun aikinsa, sai yă shafe shi. |
| 12 |
| Ko da yake ina da abin da zan faɗa muku da yawa, na gwammace ba a wasiƙa ba, amma na sa zuciya in ziyarce ku, mu yi magana baka da baka. don farin cikinmu ya zama cikakke. |
| 13 |
| 'Ya'yan 'yar'uwarki zaɓaɓɓiya suna gaishe ki. |
| Adana Bayanan kula |
https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/2john/001.mp3
1
1