× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Madurese Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Littafi Mai Tsarki 1979 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 2 Samaʼila FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 18 1234567891011121314151617181920212223241 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132331 1 1 Littafi Mai Tsarki 1979 2 Samaʼila 18 Adana Bayanan kula 1Dawuda kuwa ya shirya sojojin da suke tare da shi, sa'an nan ya naɗa musu shugabanni na dubu dubu da na ɗari ɗari.2Ya aiki runduna zuwa yaƙi. Ya sa Yowab ya shugabanci sulusi ɗaya na rundunar, sulusi na biyu kuma ya sa a hannun Abishai, ɗan Zeruya, ɗan'uwan Yowab. Sulusi na uku kuwa ya sa a hannun Ittayi Bagitte. Sa'an nan sarki ya ce wa sojojin, “Ni ma da kaina zan tafi tare da ku.”3Amma sojojin suka ce, “Ba za ka tafi tare da mu ba, gama idan muka gudu, ba za su kula da mu ba. Ko rabinmu sun mutu, ba za su kula ba, gama kai kana bakin mutum dubu goma (10,000) na mutanenmu. Zai fi kyau kuma ka zauna cikin gari ka riƙa aika mana da taimako.”4Sai sarki ya ce musu, “Duk abin da kuka ga ya fi muku kyau, shi zan yi.” Sarki kuwa ya tsaya a bakin ƙofar garin sa'ad da sojojin suke fita, kashi kashi, ɗari ɗari, da dubu dubu.5Ya kuma umarci Yowab, da Abishai, da Ittayi ya ce, “Ku lurar mini da saurayin nan, Absalom.” Dukan sojojin suka ji umarnin da sarki ya yi wa shugabanninsu a kan Absalom.6Sojojin suka tafi zuwa karkara don su yi yaƙi da mutanen Isra'ila. Suka yi yaƙin a kurmin Ifraimu.7Mutanen Isra'ila suka sha kashi a hannun jarumawan Dawuda. A wannan rana aka kashe mutane da yawa, har mutum dubu ashirin (20,000).8Yaƙin ya bazu ko'ina a ƙasar. A ranar abin da kurmin ya ci ya fi abin da aka kashe da takobi.9Absalom yana cikin gudu sai ya fāɗa a hannun jarumawan Dawuda. Sa'ad da yake cikin gudu a kan alfadarinsa, sai alfadarin ya kurɗa tsakanin rassan babban itacen oak. Kansa ya sarƙafe kam cikin rassan itacen oak ɗin, alfadarin kuwa ya wuce, ya bar shi yana rataye yana lilo.10Da wani mutum ya gani, sai ya tafi ya faɗa wa Yowab, ya ce, “Na ga Absalom yana reto a itacen oak.”11Yowab ya ce wa mutumin da ya faɗa masa, “Kai! Ka gan shi! Me ya sa ba ka buge shi har ƙasa ba? Ai, da na ba ka azurfa goma da abin ɗamara.”12Sai mutumin ya ce wa Yowab, “Ko da za a ba ni azurfa dubu a hannuna, ba zan miƙa hannuna in taɓa ɗan sarki ba, gama a kunnuwanmu sarki ya umarce ka, kai da Abishai, da Ittayi cewa, ‘Ku lura mini da saurayin nan, Absalom.’13In da na ci amana har na kashe shi, ba yadda abin zai ɓoyu ga sarki, sa'an nan kai da kanka ka zame, ka bar ni.”14Yowab ya ce, “Ba zan ɓata lokaci haka da kai ba.” Sai ya ɗibi mashi uku ya soki Absalom a ƙahon zuciya, tun yana da sauran rai, a maƙale cikin itacen oak.15Sa'an nan samari goma masu ɗaukar wa Yowab makamai, suka kewaye Absalom, suka yi ta dūkansa har ya mutu.16Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, sojoji suka komo daga runtumar Isra'ilawa. Yowab ya tsai da su.17Suka ɗauki gawar Absalom, suka jefa ta cikin wani rami mai zurfi a kurmin, suka tula tsibin duwatsu a kanta. Dukan Isra'ilawa kowa ya tsere zuwa gidansa.18Tun Absalom yana da rai ya gina wa kansa al'amudi a kwarin sarki, gama ya ce, “Ba ni da ɗa wanda zai sa a riƙa tunawa da ni.” Ya kira al'amudin da sunansa. Ana kuwa kiransa al'amudin Absalom har wa yau.19Ahimawaz ɗan Zadok ya ce wa Yowab, “Ka yarda mini in sheƙa a guje in kai wa sarki labari yadda Ubangiji ya cece shi daga hannun magabtansa.”20Yowab ya ce masa, “Ba za ka kai labari yau ba, sai wata rana ka kai, amma yau ba za ka kai labari ba, domin ɗan sarki ya mutu.”21Sa'an nan Yowab ya ce wa wani mutumin Habasha, “Tafi ka faɗa wa sarki abin da ka gani.” Sai Bahabashen ya rusuna wa Yowab, sa'an nan ya sheƙa a guje.22Ahimawaz ɗan Zadok kuma ya ce wa Yowab, “Ko mene ne zai faru dai, ka bar ni in bi bayan Bahabashen a guje.” Yowab ya ce masa, “Don me za ka tafi, ɗana, tun da yake ba za ka sami lada saboda labarin da za ka kai ba?”23Ahimawaz ya ce, “Duk dai abin da zai faru, zan tafi.” Sai Yowab ya yardar masa ya tafi. Sa'an nan Ahimawaz ya sheƙa, ya bi ta hanyar fili, ya wuce Bahabashen.24Dawuda kuwa yana zaune a tsakanin ƙofofi biyu na garin. Mai tsaro ya hau kan soron da yake kan bangon garu. Da ya ɗaga kai ya duba, sai ya ga mutum yana gudu shi kaɗai.25Ya ta da murya, ya faɗa wa sarki. Sai sarki ya ce, “Idan shi kaɗai ne, yana kawo labari ne.” Mutumin ya yi ta ƙara zuwa kusa.26Mai tsaron kuma ya ga wani mutum yana zuwa shi ma a guje, sai ya ta da murya wajen mai ƙofar garin, ya ce, “Ga wani mutum kuma yana zuwa a guje!” Sai sarki ya ce, “Shi ma labari yake kawowa.”27Mai tsaron ya ce, “Na ga gudun na farin kamar gudun Ahimawaz ɗan Zadok.” Sai sarki ya ce, “Shi mutumin kirki ne, yana kawo kyakkyawan labari ne.”28Da Ahimawaz ya zo kusa da sarki, ya ce, “Salama!” Sa'an nan ya rusuna a gaban sarki ya sunkuyar da fuska ƙasa, ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji Allahnka, wanda ya ba da mutanen da suka tayar wa ubangijina, sarki.”29Sai sarki ya ce, “Na ce dai, saurayin nan, Absalom, yana nan lafiya?” Ahimawaz ya amsa, ya ce, “A sa'ad da Yowab ya aiko ni na ga babban hargitsi, amma ban san ko mene ne ba.”30Sarki kuwa ya ce, “Koma waje ɗaya, ka tsaya.” Sai ya koma waje ɗaya ya tsaya cik.31Sai ga Bahabashe ya iso, ya ce, “Abishirinka, ya ubangijina, sarki, gama a wannan rana ta yau Ubangiji ya cece ka daga hannun waɗanda suka tayar maka.”32Sarki ya tambaye shi, “Na ce dai, saurayin nan Absalom, yana lafiya?” Bahabashen ya amsa, “Allah ya sa abokan gāban ubangijina, sarki, da duk waɗanda suka tayar maka da mugunta, su zama kamar saurayin nan.”33Sai zuciyar sarki ta tsinke, ya hau cikin ɗakin da yake kan garun ƙofar garin yana ta kuka, yana cewa, “Ya ɗana Absalom, ɗana! Wayyo, ɗana Absalom! Da ma ni ne na mutu, ba kai ba. Ya Absalom, ɗana, ɗana!”Hausa Bible 1979 @ Bible Society of Nigeria 1979 Littafi Mai Tsarki 1979 2 Samaʼila 18 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/2samuel/018.mp3 24 18