× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2010 202020101 1 1 Ibraniyawa FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 10 123456789101112131 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738391 1 1 Hausa Bible 2010 Ibraniyawa 10 Adana Bayanan kula 1To, tun da yake Shari'a ishara ce kawai ta kyawawan abubuwan da suke a gaba, ba ainihin siffarsu ba, ashe, har abada ba za ta iya kammala waɗanda suke kusatar Allah ta wurin waɗannan hadayu ba, waɗanda ake yi a kai a kai kowace shekara.2In haka ne kuwa, ashe, ba sai a daina yin hadayar ba? Da an taɓa tsarkake masu ibadar nan sarai, ai, da ba su ƙara damuwa da zunubai ba.3Amma a game da irin waɗannan hadayu, akan tuna da zunubai a kowace shekara,4domin ba mai yiwuwa ba ne jinin bijimai da na awaki ya ɗauke zunubi.5Shi ya sa da Almasihu zai shigo duniya, sai ya ce, “Hadaya da sadaka kam, ba ka so, Amma kā tanadar mini jiki.6Ba ka farin ciki da hadayar ƙonewa, da kuma hadayar kawar da zunnbai.7Sa'an nan na ce, ‘Ga ni, na zo in aikata nufinka, ya Allah,’ Kamar yadda yake a rubuce a game da ni a Littafi.”8Sa'ad da ɗazu ya ce, “Ba ka son hadaya, da sadaka, da hadayar ƙonewa, da hadayar kawar da zunubai, ba ka kuwa jin daɗinsu,” wato, irin waɗanda ake miƙawa ta hanyar Shari'a,9sai kuma ya ƙara da cewa, “Ga ni, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon ne, don yă kafa na biyun.10Ta nufin nan ne aka tsarkake mu, ta wurin miƙa jikin Yesu Almasihu hadaya sau ɗaya tak, ba ƙari.11Har wa yau kuma, kowane firist yakan tsaya a kan hidimarsa kowace rana, yana miƙa hadaya iri ɗaya a kai a kai, waɗanda har abada ba za su iya ɗauke zunubai ba.12Amma shi Almasihu da ya miƙa hadaya guda ta har abada domin kawar da zunubai, sai ya zauna a dama ga Allah,13tun daga lokacin nan yana jira, sai an sa ya take maƙiyansa.14Gama ta hadaya guda kawai ya kammala waɗanda aka tsarkake har abada.15Ruhu Mai Tsarki ma yana yi mana shaida haka, domin bayan ya ce,16“Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su, Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji, Zan sa shari'una a birnin zuciyarsu, In kuma rubuta su a allon zuciyarsu,”17sai kuma ya ƙara cewa, “Ba kuma zan ƙara tunawa da zunubansu da laifofinsu ba.”18To, a inda aka sami gafarar waɗannan, ba sauran wata hadaya domin kawar da zunubi.19Saboda haka, ya 'yan'uwa, tun da muke da amincewar shiga Wuri Mafi Tsarki, ta wurin jinin Yesu,20ta wurin sabuwar hanya, rayayyiya wadda ya buɗe mana ta labulen nan, wato jikinsa,21da yake kuma muna da Firist mai girma, mai mulkin jama'ar Allah,22sai mu matsa kusa, da zuciya ɗaya, da cikakkiyar bangaskiya tabbatacciya, da zukatunmu tsarkakakku daga mugun lamiri, jikinmu kuma wankakke da tsattsarkan ruwa.23Sai mu tsaya da ƙarfi a kan bayyana yarda ga begen nan namu, domin shi mai yin alkawarin nan amintacce ne,24mu kuma riƙa kula da juna, ta yarda za mu ta da juna a tsimi mu mu yi ƙauna da aika nagari.25Kada mu bar yin taronmu, yadda waɗansu suke yi, sai dai mu ƙarfafa wa juna zuciya, tun ba ma da kuka ga ranar nan tana kusatowa ba.26In kuwa mun ci gaba da yin zunubi da gangan, bayan mun yi na'am da sanin gaskiya, to, ba fa sauran wata hadaya domin kawar da zunubai,27sai dai matsananciyar fargabar hukunci, da kuma wuta mai tsananin zafi, wadda za ta cinye maƙiyan Allah.28Kowa ya yar da Shari'ar Musa, akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidu biyu ko uku.29To mutumin da ya raina Ɗan Allah, ya kuma tozarta jinin nan na tabbatar alkawari, wanda aka tsarkake shi da shi, har ya wulakanta Ruhun alheri, wane irin hukunci mafi tsanani kuke tsammani ya cancanta fiye da wancan?30Domin mun san shi, shi wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce, ni zan sāka.” Da kuma, “Ubangiji zai yi wa jama'arsa hukunci.”31Abu ne fa mai matuƙar bantsoro a fāɗa a cikin hukuncin Allah Rayayye.32Amma dai ku tuna, a shekarun baya, bayan da aka haskaka zukatanku, kun jure tsananin fama da shan wuya,33wata rana ana zaginku, ana ta wahalshe ku, ana wulakanta ku a gaban jama'a, wata rana kuma kuna mai da kanku ɗaya da waɗanda aka yi wa haka,34domin kun ji tausayin ɗaurarru, kun kuma yarda da daɗin rai da wason da aka yi muku, tun da yake kun sakankance kuna da mallaka mafi kyau, mai tabbata kuwa.35Saboda haka, kada ku yar da amincewar nan taku, domin tana da sakamako mai yawa.36Gama yin jimiri ya kama ku, domin bayan da kun aikata nufin Allah, ku sami abin da aka yi muku alkawari.37“Sauran lokaci kaɗan, Mai zuwan nan zai zo, ba kuwa zai yi jinkiri ba.38Amma adalina, ta wurin bangaskiya zai rayu. Amma in ya ja da baya, ba zan yi farin ciki da shi ba.”39Amma mu ba a cikin waɗanda suke ja da baya su hallaka muke ba, mu a cikin masu bangaskiya muke, mai kai mu ga ceton rayukanmu.Hausa Bible 2010 Bible Society of Nigeria © 1932/2010 Hausa Bible 2010 Ibraniyawa 10 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/hebrews/010.mp3 13 10