× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Littafi Mai Tsarki 1979 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 Ibraniyawa FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 12 123456789101112131 1 1 : 1 12345678910111213141516171819202122232425262728291 1 1 Littafi Mai Tsarki 1979 Ibraniyawa 12 Adana Bayanan kula 1Saboda haka, tun da taron shaidu masu ɗumbun yawa suka kewaye mu haka, sai mu ma mu yar da dukkan abin da ya nauyaya mana, da kuma zunubin da ya ɗafe mana, mu kuma yi tseren nan da yake gabanmu tare da jimiri,2muna zuba ido ga Yesu, shi da yake shugaban bangaskiyarmu, da kuma mai kammala ta, wanda domin farin cikin da aka sa a gabansa ya daure wa gicciye, bai mai da shi wani abin kunya ba, a yanzu kuma a zaune yake a dama ga kursiyin Allah.3Ku fa, dubi wannan da ya jure irin gābar nan da masu zunubi suka sha yi da shi, don kada ku gaji, ko kuwa ku karai.4Famarku da zunubi ba ta kai har yadda za a kashe ku ba.5Kun kuma mance da gargaɗin nan da Allah ya yi muku a kan ku 'ya'yansa ne, wato “Ya ɗana, kada ka raina horon Ubangiji, Kada kuma ka karai, in ya kwaɓe ka.6Domin Ubangiji, wanda yake ƙauna, shi yake horo, Yakan kuma hori duk ɗan da ya karɓa.”7Shan wuyar da kuke jurewa, ai, duk don horo ne. Allah ya riƙe ku, ku 'ya'yansa ne. To, wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa?8In kuwa ba ku da horo irin horon da ake yi wa kowa, to, ashe, kun zama shegu ke nan, ba 'yan halal ba.9Har wa yau kuma, ai, muna da ubanninmu na jiki da suke hore mu, mun kuwa yi musu ladabi. Ashe, ba za mu fi yi wa Uban ruhohinmu biyayya ƙwarai ba, mu rayu?10Su kam, sun hore mu a ɗan lokaci kaɗan don ganin damarsu, amma shi, don amfanin kanmu ne yake horonmu, domin mu zama abokan tarayya a cikin tsarkinsa.11Ai, kowane irin horo, a lokacin shansa, abu ne mai baƙin ciki, ba na farin ciki ba. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.12Domin wannan, ku miƙe hannuwanku da suke reto, da gwiwoyinku marasa ƙarfi.13Ku bi miƙaƙƙun hanyoyi ɗoɗar, don kada mai ɗingishi ya gulle, a maimakon ya warke.14Ku himmantu ga zaman lafiya da kowa, ku kuma zama a tsarkake, in banda shi kuwa, ba wanda zai ga Ubangiji.15Ku kula fa, kada kowa yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai ya tabbata, ya haddasa ɓarna, har ya ɓata mutane masu yawa ta haka,16kada kuma wani yă zama fasiki, ko mai sāɓon Allah, kamar isuwa, wanda ya sayar da hakkinsa na ɗan fari a kan cimaka a ɗaya tak.17Kun dai sani daga baya, da ya so yă gāji albarkar nan, sai aka ƙi shi, domin bai sami hanyar tuba ba, ko da yake ya yi ta nemanta har da hawaye.18Ai, ba ga abin da za a taɓa ne, kuka iso ba, ko wuta mai ruruwa, ko baƙin duhu duhu ƙirin, ko hadiri,19ko ƙarar ƙaho, ko wata murya, wadda har masu jin maganarta suka yi roƙo kada su ƙara ji,20don ba su iya jure umarnin da aka yi musu ba cewa, “Ko da dabba ce ta taɓa dutsen, sai a kashe ta da jifa.”21Amma ganin wannan abu da matuƙar bantsoro yake! Har ma Musa ya ce, “Ina rawar jiki don matuƙar tsoro.”22Amma ku kun iso Ɗutsen Sihiyona ne, da birnin Allah Rayayye, Urushalima ta Sama, wurin dubban mala'iku.23Kun iso taron farin ciki na kirayayyun 'ya'yan fari na Allah, waɗanda sunayensu suke a rubuce a Sama. Kun iso wurin Allah, wanda yake shi ne mai yi wa kowa shari'a, da kuma wurin ruhohin mutane masu adalci, waɗanda aka kammala.24Kun iso wurin Yesu, matsakancin sabon alkawari, da kuma wurin jinin nan na tsarkakewa, wanda yake yin mafificiyar magana fiye da na Habila.25Ku kula fa, kada ku ƙi mai maganar nan. Domin in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi ma daga Sama?26A lokacin nan muryarsa ta girgiza duniya, amma a yanzu ya yi alkawari cewa, “Har wa yau dai sau ɗaya tak, ba duniya kaɗai zan girgiza ba, amma har sama ma.”27To, wannan cewa, “Har wa yau dai sau ɗaya tak,” ya nuna kawar da abubuwan da aka girgiza, wato abubuwan da aka halitta, don abubuwan da ba sa girgizuwa su wanzu.28Saboda haka, sai mu yi godiya domin mun sami mulkin da ba ya girgizuwa, ta haka kuma mu yi wa Allah sujada abar karɓa, tare da tsoro da tsananin girmamawa,29domin Allahnmu wuta ne mai cinyewa.Hausa Bible 1979 @ Bible Society of Nigeria 1979 Littafi Mai Tsarki 1979 Ibraniyawa 12 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/hebrews/012.mp3 13 12