× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Littafi Mai Tsarki 1979 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 Yaƙub FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 1 123451 1 1 : 1 12345678910111213141516171819202122232425261 1 1 Littafi Mai Tsarki 1979 Yaƙub 1 Adana Bayanan kula 1Daga Yakubu, bawan Allah, da kuma na Ubangiji Yesu Almasihu, zuwa ga kabilan nan goma sha biyu da suke a warwatse a duniya. Gaisuwa mai yawa.2Ya ku 'yan'uwana, duk sa'ad da gwaje-gwaje iri iri suka same ku, ku mai da su abin farin ciki ƙwarai.3Domin kun san jarrabawar bangaskiyarku takan haifi jimiri.4Sai kuma jimiri ya yi cikakken aikinsa, domin ku zama kamilai cikakku kuma, ba ku gaza da kome ba.5In waninku ya rasa hikima, sai ya roƙi Allah, mai ba kowa hannu sake, ba tare da gori ba, sai kuwa a ba shi.6Amma fa sai ya roƙa da bangaskiya, ba tare da shakka ba. Don mai shakka kamar raƙuman ruwan teku yake, waɗanda iska take korawa tana tuttunkuɗawa.7Kada irin mutumin nan mai zuciya biyu, wanda bai tsai da zuciyarsa a gu ɗaya a dukan al'amuransa ba, ya sa rai da wani abu a gun Ubangiji.8Ƙasƙantaccen ɗan'uwa yă yi taƙama da ɗaukakarsa.9Mai arziki kuma yă yi alfarma da ƙasƙancinsa, gama zai shuɗe kamar hudar ciyawa.10In rana ta tāke da ƙunarta, sai ciyawa ta bushe, hudarta ta kaɗe, kyanta kuma ya gushe. Haka ma mai arziki zai gushe yana a cikin tsakiyar harkarsa.11Albarka tā tabbata ga mai jimirin gwaji, domin in ya jure gwajin, sai ya sami kambin rai, wanda Ubangiji ya yi wa masu ƙaunarsa alkawari.12Duk wanda ake jarabta, kada ya ce Allah ne yake jarabtarsa, gama ba shi yiwuwa a jarabci Allah da mugunta, shi kansa kuwa ba ya jarabtar kowa.13Amma kowane mutum yakan jarabtu in mugun burinsa ya ruɗe shi, ya kuma yaudare shi.14Mugun buri kuma in ya yi ciki, yakan haifi zunubi. Zunubi kuma in ya balaga, yakan jawo mutuwa.15Kada fa a yaudare ku, ya 'yan'uwana ƙaunatattu.16Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.17Bisa ga nufinsa ya kawo mu ta maganar gaskiya, domin mu zama kamar nunan fari na halittarsa.18Ya 'yan'uwana ƙaunatattu, ku san wannan, wato, kowa yă yi hanzarin kasa kunne, da jinkirin yin magana, da kuma jinkirin yin fushi,19don fushin mutum ba ya aikata adalci.20Saboda haka, sai ku yar da kowane irin aikin ƙazanta da ƙeta iri iri, maganar nan da aka dasa a zuciyarku, ku yi na'am da ita a cikin halin tawali'u, domin ita ce mai ikon ceton rayukanku.21Amma ku zama masu aikata maganar, ba masu ji kawai, kuna yaudarar kanku ba.22Don duk wanda yake mai jin maganar ne kawai, ba mai aikatawa ba, kamar mutum yake mai duba fuskarsa a madubi,23don yakan dubi fuskarsa ne kawai ya tafi, nan da nan kuwa sai ya mance kamanninsa.24Amma duk mai duba cikakkiyar ka'idar nan ta 'yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai ya mance ba, sai dai mai aikatawa ne ya zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake aikatawa.25In wani yana zaton shi mai addini ne, amma bai kame bakinsa ba, sai dai ya yaudari kansa, to, addinin mutumin nan na banza ne.26Addini sahihi kuma marar aibu a gaban Allah Ubanmu, shi ne a kula da gwauraye mata, da marayu a cikin ƙuntatarsu, a kuma a keɓe kai marar aibi daga duniya.Hausa Bible 1979 @ Bible Society of Nigeria 1979 Littafi Mai Tsarki 1979 Yaƙub 1 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2010/james/001.mp3 5 1