× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 2 Samaʼila FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 1 1234567891011121314151617181920212223241 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920212223242526271 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 2 Samaʼila 1 Adana Bayanan kula 1Bayan mutuwar Shawulu, Dawuda ya dawo daga karkashe Amalekawa. Sai ya zauna a Ziklag kwana biyu.2A rana ta uku sai ga wani mutum ya zo daga sansanin Shawulu da yagaggen riga da ƙura a kansa. Da ya zo wurin Dawuda sai ya fāɗi a ƙasa don yă nuna bangirma.3Dawuda ya tambaye shi ya ce, “Daga ina ka fito?” Ya amsa ya ce, “Na tsere ne daga sansanin Isra’ila.”4Dawuda ya ce, “Gaya mini, me ya faru?” Sai ya ce, “Mutane sun gudu daga yaƙi, aka kuma karkashe yawancin mutane. Shawulu da ɗansa Yonatan ma sun mutu.”5Sai Dawuda ya ce wa saurayin da ya kawo labarin, “Yaya ka san cewa Shawulu da ɗansa Yonatan sun mutu?”6Saurayin ya ce, “Ina kan dutsen Gilbowa a lokacin sai na ga Shawulu jingine a māshinsa. Kekunan yaƙi da mahayansu suna matsowa kusa da shi.7Da ya juya ya gan ni sai ya kira ni, na kuwa ce masa, ‘Ga ni?’8“Ya tambaye ni ya ce, ‘Wane ne kai?’ “Na ce, ‘Ni mutumin Amalek ne.’9“Sai ya ce mini, ‘Matso kusa ka kashe ni! Ina cikin azabar mutuwa, sai dai har yanzu ina da rai.’10“Saboda haka na matso kusa da shi na kashe shi, domin na san cewa ba zai yi rai ba, da yake ya riga ya fāɗi. Sai na cire rawanin da yake kansa, na kuma cire warwaron hannunsa, na kuwa kawo maka su duka, ranka yă daɗe!”11Sai Dawuda da dukan mutanen da suke tare da shi suka yayyage rigunarsu.12Suka yi makoki, da kuka, da azumi har yamma saboda Shawulu da ɗansa Yonatan, da saboda sojojin Ubangiji, da kuma gidan Isra’ila, gama an karkashe su a yaƙi.13Dawuda ya ce wa saurayin da ya kawo labarin, “Daga ina ka fito?” Ya ce, “Ni ɗan wani baƙo ne, mutumin Amalek.”14Dawuda ya ce masa, “Yaya ba ka ji tsoro ɗaga hannu ka hallaka shafaffe na Ubangiji ba?”15Sai Dawuda ya kira ɗaya daga cikin mutanensa ya ce, “Je ka kashe shi!” Haka kuwa ya buge shi, ya kuwa mutu.16Gama Dawuda ya riga ya ce masa, “Alhakin jininka yana bisa kanka tun da yake da bakinka ka ce, ‘Ni ne na kashe shafaffe na Ubangiji.’ ”17Dawuda ya rera wannan makoki saboda Shawulu da ɗansa Yonatan.18Ya umarta a koya wa mutanen Yahuda wannan waƙa mai suna Makokin Baka (tana a rubuce a Littafin Yashar),19“Ya Isra’ila, an kashe darajarki a kan tuddanki. Ga shi, jarumawa sun fāɗi!20“Kada a faɗe shi a Gat, kada a yi shelarsa a titunan Ashkelon, don kada ’yan matan Filistiyawa su yi murna don kada ’yan matan marasa kaciya su yi farin ciki.21“Ya duwatsun Gilbowa, kada a sāke yin ruwa ko raɓa a kanku, balle gonakin da suke ba da hatsin hadaya su ƙara bayarwa. Gama a can ne garkuwoyin manyan sojoji suka kwanta, suka kwanta a wulaƙance. Garkuwar Shawulu kuwa, ba za a ƙara shafa mata mai ba.22“Daga jinin waɗanda aka kashe, daga tsokar naman jarumi, bakan Yonatan bai juye baya ba, takobin Shawulu bai komo ba tare da gamsuwa ba.23Shawulu da Yonatan, a raye ƙaunatattu ne da kuma bansha’awa, a mace kuma ba su rabu ba. Sun fi gaggafa sauri, sun fi zaki ƙarfi.24“Ya ku ’yan matan Isra’ila, ku yi kuka saboda Shawulu, wanda ya suturta ku da jajjayen kayan ado, wanda ya yi wa rigunarku ado da zinariya.25“Jarumawa sun fāɗi a yaƙi! Ga Yonatan matacce a tuddanku.26Na yi baƙin ciki saboda kai, Yonatan ɗan’uwana; ƙaunatacce kake a gare ni. Ƙaunarka a gare ni abar al’ajabi ce, abar al’ajabi fiye da ta mace.27“Jarumawa sun fāɗi! Makaman yaƙi sun hallaka!”Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 2 Samaʼila 1 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/2samuel/001.mp3 24 1