× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Esta FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 8 123456789101 1 1 : 1 12345678910111213141516171 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Esta 8 Adana Bayanan kula 1A wannan rana, Sarki Zerzes ya ba wa Esta mallakar Haman, abokin gāban Yahudawa. Mordekai kuma ya zo gaban sarki, gama Esta ta faɗa yadda ta haɗa dangi da shi.2Sarki ya cire zobensa na hatimi, wanda ya karɓo daga Haman ya ba Mordekai. Esta kuma ta naɗa shi a kan mallakar Haman.3Esta ta sāke roƙon sarki, ta fāɗi a ƙafafunsa tana kuka. Ta roƙe shi yă kawo ƙarshen mugun shirin nan na Haman, mutumin Agag; wanda ya shirya a kan Yahudawa.4Sai sarki ya miƙa wa Esta sandan sarauta na zinariya, ta kuwa tashi ta tsaya a gabansa.5Ta ce, “In sarki ya yarda, in kuma na sami tagomashi daga gare shi, idan kuma ya gamshe shi yă yi abin da yake daidai, idan yana jin daɗina, bari a rubuta umarni a soke hukuncin saƙonin da Haman ɗan Hammedata, mutumin Agag, ya shirya ya kuma rubuta domin a hallaka Yahudawa a dukan lardunan sarki.6Gama yaya zan jure da ganin masifa ta faɗa a kan mutanena? Yaya zan jure in ga an hallaka iyalina?”7Sarki Zerzes ya amsa wa Esta da Mordekai mutumin Yahuda, “Domin Haman ya kai wa Yahudawa hari, na ba da mallakarsa ga Esta, an kuma rataye shi a wurin rataye mai laifi.8Yanzu ku rubuta wata doka, a sunan sarki, a madadin Yahudawa, yadda kuka ga ya fi kyau ku kuma hatimce ta da zoben hatimin sarki, gama babu takardar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce da zobensa da za a iya sokewa.”9Nan da nan aka kira magatakardun fada, a ranar ashirin da uku ga watan uku, wato, watan Siban. Suka rubuta dukan umarnan Mordekai ga Yahudawa, da kuma ga shugabanni, da gwamnoni, da hakiman larduna 127 tun daga Indiya har zuwa Kush. Aka rubuta waɗannan umarnan a rubutun kowane lardi, da kuma cikin harshen kowane mutane. Aka kuma rubuta ga Yahudawa a rubutunsu da harshensu.10Mordekai ya yi rubutu da sunan Sarki Zerzes, ya hatimce saƙonin da zoben hatimin sarki, ya kuma aika da su ta hannun masu ’yan aika a kan dawakai, waɗanda sukan hau dawakai masu gudu sosai, da aka yi kiwonsu musamman saboda sarki.11Dokar sarki ta ba wa Yahudawa a kowace birni izini su taru, su kuma kāre kansu, domin su hallaka, su kashe, su kuma hallaka kowace ƙungiyar mayaƙa, na kowace ƙasa, ko lardi, da wataƙila za su kai musu, da matansu, da yaransu hari; su kuma washe mallakar abokan gābansu.12Ranar da aka shirya domin Yahudawa su yi wannan a dukan lardunan Sarki Zerzes, ita ce ranar goma sha uku ga watan goma sha biyu, wato, watan Adar.13Za a ba da kofi na rubutacciyar dokar a matsayin ƙa’ida a kowane lardi, a kuma sanar wa mutanen kowace ƙasa, domin Yahudawa su zauna da shiri a ranar, domin su ɗau fansa a kan maƙiyansu.14’Yan aikan, a kan dawakan fada, suka fita a guje, umarnin sarki yana iza su. Aka kuma ba da dokar a mazaunin masarauta wadda take Shusha.15Mordekai kuwa ya fita a gaban sarki da rigunan sarauta, masu ruwan shuɗi, da fari, da babban kambi na zinariya, da alkyabba ta lilin mai ruwan shunayya. Aka yi sowa don murna a birnin Shusha.16Ga Yahudawa kuwa, lokaci ne na murna da farin ciki, da jin daɗi da bangirma.17A kowane lardi da kowace birni, ko’ina da dokar sarki ta kai, aka yi farin ciki a cikin Yahudawa, cike da bukukkuwa. Yawan mutane da waɗansu ƙasashe suka zama Yahudawa, don tsoron Yahudawa ya kama su.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Esta 8 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/esther/008.mp3 10 8