× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Zabura FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 104 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738394041424344454647484950515253545556575859606162636465666768697071727374757677787980818283848586878889909192939495969798991001011021031041051061071081091101111121131141151161171181191201211221231241251261271281291301311321331341351361371381391401411421431441451461471481491501 1 1 : 1 12345678910111213141516171819202122232425262728293031323334351 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Zabura 104 Adana Bayanan kula 1Yabi Ubangiji, ya raina. Ya Ubangiji Allahna, kana da girma ƙwarai; kana saye da daraja da ɗaukaka.2Ubangiji ya naɗe kansa da haske kamar riga ya shimfiɗa sammai kamar tenti3ya kafa ginshiƙan ɗakin samansa a kan ruwaye. Ya maido da gizagizai suka zama keken yaƙinsa yana hawa a kan fikafikan iska.4Ya mai da iska suka zama ’yan saƙonsa harsunan wuta kuma bayinsa.5Ya kafa duniya a kan tussanta; ba za a iya matsar da ita ba.6Ka rufe ta da zurfi kamar da riga ruwaye sun tsaya a bisa duwatsu.7Amma a tsawatawarka ruwaye suka gudu da jin ƙarar tsawanka suka ruga da gudu;8suka gudu a bisa duwatsu, suka gangara zuwa cikin kwaruruka, zuwa wurin da ka shirya musu.9Ka kafa iyakar da ba a iya tsallakawa; ba za su ƙara rufe duniya ba.10Ya sa maɓulɓulai suka zuba ruwa cikin kwaruruka; yana gudu tsakanin duwatsu.11Suna ba da ruwa ga dukan namun jeji; jakunan jeji suna kashe ƙishirwansu.12Tsuntsaye sarari suna sheƙunansu kusa da ruwan; suna rera cikin rassa.13Yana wa duwatsu banruwa daga ɗakinsa na sama; ƙasa tana ƙoshiya da amfanin aikinsa.14Yana sa ciyawa tă yi girma saboda shanu, tsire-tsire domin mutum ya nome, suna fid da abinci daga ƙasa,15ruwan inabi yakan sa zuciyar mutum tă yi murna, mai kuwa yakan sa fuska tă yi haske, abinci kuma da yake riƙe zuciyarsa.16Ana yi wa itatuwan Ubangiji banruwa sosai, al’ul na Lebanon da ya shuka.17A can tsuntsaye suke sheƙunnansu; shamuwa tana da gidanta a itatuwan fir.18Manyan duwatsu na awakin jeji ne; tsagaggun duwatsun mafaka ne ga rema.19Wata ne ke ƙididdigar lokuta, rana kuma ta san sa’ad da za tă fāɗi.20Ka yi duhu, sai ya zama dare, sai dukan namun jeji a kurmi suka fito a maƙe.21Zakoki sun yi ruri sa’ad da suke farauta suna kuma neman abincinsu daga Allah.22Rana ta fito, sai suka koma shiru; suka koma suka kwanta a kogwanninsu.23Mutum yakan tafi aikinsa, zuwa wurin aikinsa har yamma.24Ina misalin yawan aikinka, ya Ubangiji! Cikin hikima ka yi su duka; duniya ta cika da halittunka.25Akwai teku, babba da kuma fāɗi, cike da halittun da suka wuce ƙirga, abubuwa masu rai babba da ƙarami.26A can jiragen ruwa suna kai komo, kuma dodon ruwan da ka yi, yă yi wasa a can.27Waɗannan duka suna dogara gare ka don ka ba su abincinsu a daidai lokaci.28Sa’ad da ba su da shi, sai su tattara shi; sa’ad da ka buɗe hannunka, sukan ƙoshi da abubuwa masu kyau.29Sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai su razana; sa’ad da ka ɗauke numfashinsu, sai su mutu su kuma koma ga ƙura.30Sa’ad da ka aika da Ruhunka, sai su halittu, su kuma sabunta fuskar duniya.31Bari ɗaukakar Ubangiji ta dawwama har abada; bari Ubangiji yă yi farin ciki cikin aikinsa,32shi wanda ya dubi duniya, sai ta razana, wanda ya taɓa duwatsu, sai suka yi hayaƙi.33Zan rera ga Ubangiji dukan raina; zan rera yabo ga Allahna muddin ina raye.34Bari tunanina yă gamshe shi, yayinda nake farin ciki a cikin Ubangiji.35Amma bari masu zunubi su ɓace daga duniya mugaye kuma kada a ƙara ganinsu. Yabi Ubangiji, ya raina. Yabi Ubangiji.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Zabura 104 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/104.mp3 150 104