× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Zabura FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 105 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738394041424344454647484950515253545556575859606162636465666768697071727374757677787980818283848586878889909192939495969798991001011021031041051061071081091101111121131141151161171181191201211221231241251261271281291301311321331341351361371381391401411421431441451461471481491501 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738394041424344451 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Zabura 105 Adana Bayanan kula 1Ku yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; ku sanar a cikin al’ummai abin da ya yi.2Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi; ku faɗa dukan abubuwan mamakin da ya aikata.3Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki; bari zukatan waɗanda suke neman Ubangiji su yi farin ciki.4Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa; ku nemi fuskarsa kullum.5Ku tuna da abubuwan mamakin da ya yi, mu’ujizansa, da kuma hukunce-hukuncen da ya zartar,6Ya ku zuriyar Ibrahim bawansa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub, zaɓaɓɓensa.7Shi ne Ubangiji Allahnmu; kuma hukunce-hukuncensa suna a cikin dukan duniya.8Yana tuna da alkawarinsa har abada, maganar da ya umarta, har tsararraki dubu,9alkawarin da ya yi da Ibrahim, rantsuwar da ya yi wa Ishaku.10Ya tabbatar da shi ga Yaƙub a matsayin ƙa’ida, Isra’ila a matsayin madawwamin alkawari,11“Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana a matsayin rabo za ka yi gādo.”12Sa’ad da suke kima kawai, kima sosai, da kuma baƙi a cikinta,13suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma, daga masarauta zuwa wata.14Bai bar kowa yă danne su ba; saboda su, ya tsawata wa sarakuna,15“Kada ku taɓa shafaffena; kada ku yi wa annabawa lahani.”16Ya sauko da yunwa a kan ƙasa ya kuma lalace dukan tanadinsu na abinci;17ya kuma aiki mutum a gabansu, Yusuf, da aka sayar a matsayin bawa.18Suka raunana ƙafafunsa da sarƙa aka sa wuyansa cikin ƙarafa,19sai abin da ya rigafaɗi ya cika sai da maganar Ubangiji ta tabbatar da shi mai gaskiya.20Sarki ya aika aka kuma sake shi, mai mulkin mutane ya ’yantar da shi.21Ya mai da shi shugaban gidansa, mai mulki a bisa dukan abin da ya mallaka,22don yă umarci sarakunansa yadda ya ga dama yă kuma koya wa dattawa hikima.23Sa’an nan Isra’ila ya shiga Masar; Yaƙub ya yi zama kamar baƙo a ƙasar Ham.24Ubangiji ya mai da mutanensa suka yi ta haihuwa; ya sa suka yi yawa suka fi ƙarfin maƙiyansu,25waɗanda ya juya zukatansu su ƙi mutanensa don su haɗa baki a kan bayinsa.26Ya aiki Musa bawansa, da Haruna, wanda ya zaɓa.27Suka yi mu’ujizansa a cikinsu, abubuwan mamakinsa a cikin ƙasar Ham.28Ya aiko da duhu ya kuma sa ƙasar tă yi duhu, ba domin sun yi tawaye a kan maganarsa ba?29Ya mai da ruwaye suka zama jini, ya sa kifayensu suka mutu.30Ƙasarsu ta yi ta fid da kwaɗi, waɗanda suka haura cikin ɗakunan kwana na masu mulkinsu.31Ya yi magana, sai tarin ƙudaje suka fito, cinnaku kuma ko’ina a ƙasar.32Ya mai da ruwan samansu ya zama ƙanƙara, da walƙiya ko’ina a ƙasarsu;33ya lalace inabinsu da itatuwan ɓaurensu ya ragargaza itatuwan ƙasarsu.34Ya yi magana, sai fāri ɗango suka fito, fāran da ba su ƙidayuwa;35suka cinye kowane abu mai ruwan kore a cikin ƙasarsu, suka cinye amfanin gonarsu36Sa’an nan ya karkashe dukan ’yan fari a cikin ƙasarsu, nunan fari na dukan mazantakarsu.37Ya fitar da Isra’ila, ɗauke da azurfa da zinariya, kuma daga cikin kabilansu babu wani da ya kāsa.38Masar ta yi murna sa’ad da suka tafi, saboda tsoron Isra’ila ya fāɗo musu.39Ya shimfiɗa girgije kamar mayafi, da kuma wuta don ta ba su haske da dare.40Suka roƙa, ya kuwa ba su makware ya kuma ƙosar da su da abinci daga sama.41Ya buɗe dutse, sai ruwa ya ɓulɓulo, kamar kogi ya gudu zuwa cikin hamada.42Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki da ya ba wa bawansa Ibrahim.43Ya fitar da mutanensa da farin ciki, zaɓaɓɓunsa da sowa ta farin ciki;44ya ba su ƙasashen al’ummai, suka kuma sami gādon abin da waɗansu sun sha wahala a kai,45don su kiyaye farillansa su kuma kiyaye dokokinsa. Yabo ga Ubangiji.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Zabura 105 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/105.mp3 150 105