× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Zabura FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 106 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738394041424344454647484950515253545556575859606162636465666768697071727374757677787980818283848586878889909192939495969798991001011021031041051061071081091101111121131141151161171181191201211221231241251261271281291301311321331341351361371381391401411421431441451461471481491501 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738394041424344454647481 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Zabura 106 Adana Bayanan kula 1Yabi Ubangiji. Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.2Wane ne zai furta manyan ayyukan Ubangiji ko yă furta cikakken yabonsa?3Masu albarka ne waɗanda suke yin adalci, waɗanda kullum suke yin abin da yake daidai.4Ka tuna da ni, ya Ubangiji, sa’ad da ka nuna alheri ga mutanenka, ka zo ka taimake ni sa’ad da ka cece su,5don in ji daɗin nasarar zaɓaɓɓunka, don in sami rabo cikin farin cikin al’ummarka in kuma shiga gādonka cikin yin yabo.6Mun yi zunubi, kamar yadda kakanninmu suka yi; mun yi ba daidai ba muka kuma aikata mugunta.7Sa’ad da kakanninmu suke a Masar, ba su damu da mu’ujizanka ba; ba su tuna yawan alheranka ba, suka kuma yi tayarwa a teku, Jan Teku.8Duk da haka ya cece su saboda sunansa, don yă sanar da ikonsa mai girma.9Ya tsawata wa Jan Teku, ya kuwa bushe; ya bi da su ta cikin zurfafa sai ka ce a hamada.10Ya cece su daga hannun maƙiyi; daga hannun abokin gāba ya fanshe su.11Ruwaye suka rufe abokan gābansu; babu ko ɗaya da ya tsira.12Sa’an nan suka gaskata alkawarinsa suka kuma rera yabonsa.13Amma nan da nan suka manta abin da ya yi ba su kuwa jira shawararsa ba.14A cikin hamada suka bar sha’awarsu ta mamaye su a ƙasar da babu kome suka gwada Allah.15Sai ya ba su abin da suka roƙa, amma ya aika musu da muguwar cuta.16A sansani suka ji kishin Musa da kuma Haruna, wanda Ubangiji ya keɓe.17Ƙasa ta buɗe ta haɗiye Datan ta binne iyalin Abiram.18Wuta ta ƙuno a cikin mabiyansu; harshen wuta ya cinye mugaye.19A Horeb suka yi ɗan maraƙi suka yi wa gunkin zubi daga ƙarfe sujada.20Suka sauke Ɗaukakarsu saboda siffar bijimi, wanda yake cin ciyawa.21Suka manta da Allahn da ya cece su, wanda ya aikata manyan abubuwa a Masar,22mu’ujizai a ƙasar Ham ayyukan banrazana a Jan Teku.23Don haka ya ce zai hallaka su, amma Musa, zaɓaɓɓensa, ya yi godo a gabansa don yă kau da hasalarsa daga hallaka su.24Sai suka rena ƙasa mai ni’ima; ba su gaskata alkawarinsa ba.25Suka yi gunaguni a tentunansu ba su kuwa yi biyayya da Ubangiji ba.26Saboda haka ya rantse musu ya kuma ɗaga hannu cewa zai sa su mutu a cikin hamada,27ya sa zuriyarsu su mutu a cikin al’ummai ya kuma watsar da su cikin dukan ƙasashe.28Suka haɗa kai da Ba’al-Feyor suka kuma ci hadayun da aka miƙa wa allolin da ba su da rai;29suka tsokane Ubangiji ya yi fushi ta wurin mugayen ayyukansu, sai annoba ta ɓarke a cikinsu.30Amma Finehas ya miƙe tsaye ya ɗauki mataki, sai annobar ta daina.31An ayana masa wannan a matsayin adalci har zamanai marar matuƙa masu zuwa.32A ruwan Meriba suka ba Ubangiji fushi, sai wahala ta zo wa Musa saboda su;33saboda sun yi tayarwa a kan Ruhun Allah, har mugayen kalmomi suka fito daga leɓunan Musa.34Ba su hallakar da mutanen yadda Ubangiji ya umarce su ba,35amma suka yi cuɗanya da al’ummai suka ɗauki al’adunsu.36Suka yi wa gumakansu sujada, waɗanda suka zama tarko gare su.37Suka miƙa ’ya’yansu maza hadaya ’yan matansu kuma ga aljanu.38Suka zub da jini marar laifi, jinin ’ya’yansu maza da mata, waɗanda suka miƙa hadaya ga gumakan Kan’ana, ƙasar kuwa ta ƙazantu ta wurin jininsu.39Suka ƙazantar da kansu ta wurin abin da suka yi; ta wurin ayyukansu suka yi karuwanci.40Saboda haka Ubangiji ya yi fushi da mutanensa ya ji ƙyamar gādonsa.41Ya miƙa su ga al’ummai, maƙiyansu kuma suka yi mulki a kansu.42Abokan gābansu suka danne su suka sa su a ƙarƙashin ikonsu.43Sau da yawa ya cece su, amma sun nace su yi tawaye suka kuma lalace cikin zunubinsu.44Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu;45saboda su ya tuna da alkawarinsa kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi.46Ya sa aka ji tausayinsu a wurin dukan waɗanda suka kame su.47Ka cece mu, Ubangiji Allahnmu, ka kuma tattara mu daga al’ummai, don mu yi wa sunanka mai tsarki godiya mu kuma ɗaukaka cikin yabonka.48Yabo ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, daga madawwami zuwa madawwami. Bari dukan mutane su ce, “Amin!” Yabo ga Ubangiji.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Zabura 106 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/106.mp3 150 106