× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Zabura FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 69 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738394041424344454647484950515253545556575859606162636465666768697071727374757677787980818283848586878889909192939495969798991001011021031041051061071081091101111121131141151161171181191201211221231241251261271281291301311321331341351361371381391401411421431441451461471481491501 1 1 : 6 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435361 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Zabura 69 Adana Bayanan kula 1Ka cece ni, ya Allah, gama ruwa ya kai wuyata2Na nutse cikin laka mai zurfi, inda babu wurin tsayawa. Na shiga cikin ruwaye masu zurfi; rigyawa ya sha kaina.3Na gaji da kira ina neman taimako; maƙogwarona ya bushe idanuna sun dushe, suna neman Allahna.4Waɗanda suke ƙina ba dalili sun fi gashin kaina yawa; da yawa ne abokan gābana babu dalili, su da suke nema su hallaka ni. An tilasta mini in mayar da abin da ban sata ba.5Ka san wautata, ya Allah; laifina ba a ɓoye yake daga gare ka ba.6Bari waɗanda suke sa zuciya gare ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki; bari waɗanda suke neman ka kada su sha kunya saboda ni, Ya Allah na Isra’ila.7Gama na jimre da ba’a saboda kai, kunya kuma ta rufe fuskata.8Ni baƙo ne a cikin ’yan’uwana, bare kuma ga ’ya’yan mahaifiyata maza;9gama himma da nake yi wa gidanka yana ƙunata, kuma zagi na masu zaginka yana fāɗuwa a kaina.10Sa’ad da na yi kuka na kuma yi azumi dole in jimre da ba’a;11sa’ad da na sanya rigunan makoki, mutane suna maishe ni abin dariya.12Masu zama a ƙofa suna mini ba’a, na zama waƙa a bakin bugaggu da giya.13Amma na yi addu’a gare ka, ya Ubangiji, a lokacin da ka ga dama; a cikin ƙaunarka mai girma, ya Allah, ka amsa mini da tabbacin ceto.14Ka fid da ni daga laka, kada ka bari in nutse; ka cece ni daga waɗanda suke ƙina, daga rurin ruwaye.15Kada ka bar rigyawa yă sha kaina ko zurfafa su haɗiye ni ko rami yă rufe bakinsa a kaina.16Ka amsa mini, ya Ubangiji cikin alherin ƙaunarka; cikin jinƙanka mai girma ka juyo gare ni.17Kada ka ɓoye fuskarka daga bawanka; ka amsa mini da sauri, gama ina cikin wahala.18Ka zo kusa ka kuɓutar da ni; ka fanshe ni saboda maƙiyana.19Ka san yadda ake mini ba’a, ake kunyatar da ni da kuma yadda nake shan kunya; dukan abokan gābana suna a gabanka.20Ba’a ta sa zuciyata ta karai ta bar ni ba mataimaki; Na nemi a ji tausayina, amma ban sami ko ɗaya ba, na nemi masu ta’aziyya, amma ban sami ko ɗaya ba.21Sun sa abin ɗaci cikin abincina suka kuma ba ni ruwan inabi mai tsami sa’ad da nake jin ƙishi.22Bari teburin da aka shirya a gabansu yă zama musu tarko; bari yă zama sakamakon laifi da kuma tarko.23Bari idanunsu yă dushe don kada su gani, bayansu kuma yă tanƙware har abada.24Ka kwarara fushinka a kansu; bari fushinka mai zafi yă ci musu.25Bari wurinsu yă zama kufai; kada ka bar wani yă zauna a tentunansu.26Gama sun tsananta wa waɗanda ka hukunta suna kuma taɗin wahalar waɗanda ka ji musu rauni.27Ka neme su da laifi a kan laifi; kada ka bar su su sami rabo a cikin cetonka.28Bari a shafe su sarai daga littafin rai kada a kuma lissafta su tare da adalai.29Ina cikin zafi da kuma azaba; bari cetonka, ya Allah, yă tsare ni.30Zan yabe sunan Allah cikin waƙa in kuma ɗaukaka shi tare wurin yin godiya.31Wannan zai gamshi Ubangiji fiye da saniya, fiye da bijimi da ƙahoninsa da kuma kofatansa.32Matalauta za su gani su kuma yi murna, ku da kuke neman Allah, bari zukatanku su rayu!33Ubangiji yakan ji masu bukata ba ya kuwa ƙyale kamammun mutanensa.34Bari sama da ƙasa su yabe shi, tekuna da dukan abin da yake motsi a cikinsu,35gama Allah zai cece Sihiyona yă sāke gina biranen Yahuda. Sa’an nan mutane za su zauna a can su mallake ta,36’ya’yan bayinsa za su gāje ta, waɗanda kuma suna ƙaunar sunansa za su zauna a can.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Zabura 69 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/psalms/069.mp3 150 69