× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Karin Magana FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 27 123456789101112131415161718192021222324252627282930311 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920212223242526271 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Karin Magana 27 Adana Bayanan kula 1Kada ka yi fariya a kan gobe gama ba san abin da ranar za tă kawo ba.2Ka bar wani ya yabe ka, ba kai kanka ba; wani dabam, ba leɓunanka ba.3Dutse yana da nauyi yashi kuma wahala ce, amma tsokanar wawa ta fi su duka nauyi.4Fushi mugun abu ne mai hallakarwa, amma wa zai iya tsaya a gaban kishi?5Gara tsawatawar da ake yi a fili da ƙaunar da ake yi a ɓoye.6Za a iya amince da rauni daga aboki, amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!7Duk wanda ya ƙoshi da zuma, ba ya marmarinsa kuma amma wanda yake yunwa ko abin da yake da ɗaci ma zai ji shi da zaƙi.8Kamar tsuntsun da ya ɓace daga sheƙarsa haka yake da mutumin da ya bar gidansa.9Man shafawa mai ƙanshi da kuma turare kan faranta zuciya, gaisuwar amini kuma takan fito daga shawarar kirki.10Kada ka manta da abokinka da kuma abokin mahaifinka, kuma kada ka tafi gidan ɗan’uwanka sa’ad da masifa ta same ka, gara ka je wurin maƙwabci na kusa da ka je wurin ɗan’uwan da yake da nisa.11Ka zama mai hikima, ɗana, ka kuma faranta mini zuciya; zan iya amsa kowace irin suƙar da wani zai yi mini.12Mai basira kan hango hatsari ya kuma kauce, marar azanci zai yi ta kutsa kai ciki, daga baya ya yi da na sani.13A karɓe rigunan wanda ya ɗauki lamunin baƙo; a riƙe shi jingina in ya yi shi don mace marar aminci.14In mutum ya albarkaci maƙwabcinsa da murya mai ƙarfi da sassafe, za a ɗauka shi a matsayin la’ana.15Mace mai fitina kamar ɗiɗɗigar ruwa take ba ƙaƙƙautawa;16hana ta yana kamar yin ƙoƙari tsai da iska ne ko yin ƙoƙarin cafke mai a tafin hannunka.17Kamar yadda ƙarfe kan wasa ƙarfe haka mutum kan koyi daga mutum.18Duk wanda ya lura da itacen ɓaure, zai ci ’ya’yansa, kuma duk wanda ya lura da maigidansa za a girmama shi.19Kamar yadda ruwa kan nuna yadda fuska take, haka zuciyar mutum kan nuna irin mutumin.20Mutuwa da Hallaka ba sa ƙoshi, haka idanun mutum ba sa ƙoshi da gani.21Ana gwajin azurfa da kuma zinariya da wuta, amma akan gwada mutum ta wurin yabon da ya samu.22Ko da ka daka wawa a turmi, kana daka shi kamar hatsi da taɓarya, ba za ka fid da wauta daga gare shi ba.23Ka tabbata ka san lafiyar garken tumakinka, ka mai da hankali ga garken shanunka;24domin dukiya ba ta dawwama har abada, ba a kuma kasance da rawani daga tsara zuwa tsara.25Sa’ad da aka yanki ingirci sabon toho kuma ya bayyana aka kuma tattara ciyawa daga tuddai,26gashin raguna za su tanada maka tufafi, za ka iya sayi gonaki masu kyau da kuɗin awaki.27Za ka kasance da madarar awaki mai yawa don ka ciyar da kanka da kuma iyalinka ka kuma inganta bayinka mata.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Karin Magana 27 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/proverbs/027.mp3 31 27