× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 Ishaya FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 30 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738394041424344454647484950515253545556575859606162636465661 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132331 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Ishaya 30 Adana Bayanan kula 1“Kaiton ’ya’ya masu tayarwa,” in ji Ubangiji, “ga waɗanda suke ƙulle-ƙullen da ba nawa ba, suna yin yarjejjeniya, amma ba ta Ruhuna ba, suna jibga zunubi a kan zunubi;2waɗanda suka gangara zuwa Masar ba tare da sun nemi shawarata; waɗanda suke neman taimakon kāriyar Fir’auna, don neman inuwar mafakar Masar.3Amma kāriyar Fir’auna za tă zama muku abin kunya, inuwar Masar za tă jawo muku kunya.4Ko da yake suna da shugabanni a Zowan kuma jakadunsu sun iso Hanes,5kowa zai sha kunya saboda mutanen da ba su da amfani gare su, waɗanda ba sa taimako ko amfani, sai dai jawo kunya da da-na-sani.”6Allah ya faɗa game da dabbobin Negeb cewa, Ta cikin ƙasa mai wahala da mai hatsari inda zakoki da zakanya, inda macizai masu dafi da macizai masu tashi sama suke, jakadu na ɗaukan arzikinsu a kan jakuna, dukiyarsu a kan raƙuma, zuwa ƙasan nan marar riba,7zuwa Masar, wadda taimakonta marar amfani ne. Saboda haka na yi mata laƙabi Rahab Marar Yin Kome.8Tafi yanzu, ka rubuta musu a kan allo, ka rubuta shi a kan littafi, cewa kwanaki suna zuwa zai zama madawwamin shaida.9Waɗannan mutane masu tawaye, ’ya’ya masu ruɗu, ’ya’yan da ba sa niyya su saurara ga umarnan Ubangiji.10Sukan ce wa masu gani, “Kada ku ƙara ganin wahayi!” Ga annabawa kuwa sukan ce, “Kada ku ƙara ba mu wahayin abin da yake daidai! Faɗa mana abubuwan da muke so mu ji ne kawai, ku yi annabcin abin da zai ruɗe mu.11Ku bar wannan hanya, ku tashi daga wannan hanya, ku kuma daina kalubalantarmu da Mai Tsarkin nan na Isra’ila!”12Saboda haka, ga abin da Mai Tsarkin nan na Isra’ila yake cewa, “Saboda haka kun ƙi wannan saƙo, kuka dogara ga aikin kama-karya kuka kuma dogara ga yin ruɗu,13wannan zunubi zai zama muku kamar bango mai tsayi, tsagagge da yake kuma fāɗuwa, da zai rushe nan da nan, ba tsammani.14Zai rushe kucu-kucu kamar tukunyar yumɓu, ya ragargaje ƙaf har cikin gutsattsarinsa ba za a sami ko ɗan katanga don ɗiba garwashin wuta ko a ɗiba ruwa daga tanki ba.”15Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka, Mai Tsarkin nan na Isra’ila ya faɗa, “Cikin tuba da hutu ne kaɗai cetonku yake, cikin shiru da dogara gare ni ne za ku sami ƙarfinku, amma ba za ku sami ko ɗaya a cikinsu ba.16Kun ce, ‘A’a, za mu gudu a kan dawakai.’ Saboda haka za ku gudu! Kun ce, ‘Za mu hau dawakai masu sauri mu gudu.’ Saboda haka masu fafararku za su fi ku gudu!17Dubu za su gudu don barazanar mutum guda; da jin barazanar mutane biyar dukanku za ku yi ta gudu sai an bar ku kamar sandar tuta a kan dutse, kamar tuta a kan tudu.”18Duk da haka Ubangiji yana marmari ya yi muku alheri; ya tashi don yă nuna muku jinƙai. Gama Ubangiji Allah ne mai aikata gaskiya. Masu albarka ne dukanku waɗanda suke dogara gare shi!19Ya mutanen Sihiyona, waɗanda suke zama a Urushalima, ba za ku ƙara kuka ba. Zai zama mai alheri sa’ad da kuka yi kukan neman taimako! Da zarar ya ji, zai amsa muku.20Ko da yake Ubangiji yakan ba da abincin azaba da ruwan wahala, ba za a ƙara ɓoye malamanku ba; da idanunku za ku gan su.21Ko kun juye dama ko hagu, kunnuwanku za su ji murya a bayanku tana cewa, “Ga hanya; ku yi tafiya a kai.”22Sa’an nan za ku ƙazantar da gumakanku da kuka dalaye da zinariya; za ku zubar da su kamar rigar al’adar mace ku kuma ce musu, “Ku ɓace mana da gani!”23Zai kuma aiko muku da ruwan sama don shuki a ƙasa, kuma abincin da zai fito daga gona zai zama mai albarka da kuma mai yawa. A wannan rana shanu za su yi kiwo a wadatacciyar makiyaya.24Shanunku da jakunanku da suke huɗar gonakinku za su ci harawa mafi kyau, wanda an sheƙe shi da babban cokali mai yatsu da kuma babban cokali.25A ranar babban kisa, sa’ad da hasumiyoyi za su fāɗi, rafuffukan ruwa za su malalo a kan kowane dutse da kowane tudu mai tsawo.26Wata zai yi haske kamar rana, kuma hasken rana zai ma yi sau bakwai na haskenta, kamar hasken cikakku ranaku bakwai, sa’ad da Ubangiji zai ɗaura raunukan mutanensa ya kuma warkar da raunukan da ya yi musu.27Duba, Sunan Ubangiji yana zuwa daga nesa, tare da fushi mai ƙuna da kuma baƙin hayaƙi; leɓunansa sun cika da fushi, harshensa kuma wuta ce mai cinyewa.28Numfashinsa kamar raƙuman ruwa masu gudu yana tashi har zuwa wuya. Yakan tankaɗe al’ummai cikin lariyar hallaka; yakan sa a muƙamuƙan mutane linzamin da zai jagorance su su kauce.29Za ku kuma rera kamar a daren da kuke shagalin biki mai tsarki; zukatanku za su yi farin ciki kamar sa’ad da mutane sukan haura da busa zuwa dutsen Ubangiji, zuwa Dutse na Isra’ila.30Ubangiji zai sa mutane su ji muryarsa mai daraja ya kuma sa su ga hannunsa na saukowa tare da fushi mai ƙuna da kuma wuta mai cinyewa, gizagizai za su ɓarke, za a yi hadarin tsawa da ƙanƙara.31Muryar Ubangiji za tă firgita Assuriya da sandar mulkinsa zai kashe su.32Kowane bugun da Ubangiji zai yi musu da bulalarsa na hukunci zai zama kiɗi ga ganguna da garaya, yayinda yake yaƙi da su da naushin hannunsa.33An riga an shirya wurin ƙonawa; an shirya shi saboda sarki. An haƙa ramin wutarsa da zurfi da kuma fāɗi, da isashen wuta da itacen wuta; numfashin Ubangiji, yana kamar kibiritu mai ƙuna, da aka sa masa wuta.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Sabon Rai Don Kowa 2020 Ishaya 30 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/isaiah/030.mp3 66 30