× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Ishaya FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 59 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738394041424344454647484950515253545556575859606162636465661 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920211 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Ishaya 59 Adana Bayanan kula 1Tabbatacce hannun Ubangiji bai kāsa yin ceto ba, kunnensa kuma bai kurmance da zai kāsa ji ba.2Amma laifofinku sun raba ku da Allahnku; zunubanku sun ɓoye fuskarsa daga gare ku, saboda kada yă ji.3Gama hannuwanku sun ƙazantu da jini, yatsotsinku kuma da alhaki. Leɓunanku suna faɗin ƙarairayi, harshenku kuma yana raɗar mugayen abubuwa.4Babu wani mai ce a yi adalci; babu wani mai nema a dubi al’amarinsa da mutunci. Sun dogara a gardandamin banza suna ƙarairayi; suna ɗaukar cikin ɓarna, su haifi mugunta.5Suna ƙyanƙyashe ƙwan kāsā su kuma saƙa yanar gizo-gizo. Duk wanda ya ci ƙwansu zai mutu, kuma sa’ad da ƙwan ya fashe, zai ƙyanƙyashe kububuwa.6Yanar gizo-gizonsu ba amfani don tufa; ba za su iya rufuwa da abin da suka yi ba. Ayyukansu mugaye ne, ayyukan tā da hargitsi kuma suna a hannuwansu.7Ƙafafunsu sukan gaggauta zuwa aikata zunubi; suna da saurin zub da jini. Tunaninsu mugaye ne; lalaci da hallaka sun shata hanyoyinsu.8Ba su san hanyar salama ba; babu adalci a hanyoyinsu. Sun mai da su karkatattun hanyoyi; babu wanda zai yi tafiya a kansu ya sami salama.9Saboda haka gaskiya ta yi nisa da mu, adalci kuma ba ya kaiwa gare mu. Muna neman haske, sai ga duhu; muna neman haske, sai muka yi ta tafiya cikin baƙin inuwa.10Kamar makafi, sai lallubar bango muke yi, muna lallubawar hanyarmu kamar marasa idanu. Da tsakar rana muna tuntuɓe sai ka ce wuri ya fara duhu; cikin ƙarfafa, mun zama kamar matattu.11Muna gurnani kamar beyar; muna ta ƙugi kamar kurciyoyi. Muna ta neman adalci amma ina; mun nemi fansa, amma yana can da nisa.12Gama laifofinmu suna da yawa a gabanka, zunubanmu kuma suna ba da shaida gāba da mu. Laifofinmu kullum suna a gabanmu, muna kuma sane da laifofinmu,13tawaye da mūsun Ubangiji, mun juye bayanmu ga Allahnmu, zugawa a yi zalunci da tayarwa, faɗin ƙarairayi da zukatanmu suka shirya.14Saboda haka aka kau da yin gaskiya adalci kuma ya tsaya can da nesa; gaskiya ta yi tuntuɓe a tituna, sahihanci ba zai shiga ba.15Gaskiya ta ɓace gaba ɗaya, kuma duk wanda ya guji mugunta zai zama ganima. Ubangiji ya duba bai kuwa ji daɗi cewa babu adalci ba.16Ya ga cewa babu wani, ya yi mamaki cewa babu wanda zai shiga tsakani; saboda haka hannunsa ya aikata masa ceto, adalcinsa kuma ya raya shi.17Ya yafa sulke a matsayin rigar ƙirji, da hulan kwanon ceto a kansa; ya sa rigunan ɗaukar fansa ya kuma nannaɗe kansa da kishi kamar a cikin alkyabba.18Bisa ga abin da suka yi, haka za a sāka fushi a kan abokan gābansa ramuwa kuma a kan maƙiyansa; zai sāka wa tsibirai abin da ya dace da su.19Daga yamma, mutane za su ji tsoron Ubangiji, daga mafitar rana kuma, za su girmama ɗaukakarsa. Gama zai zo kamar rigyawa mai tsananin gudu cewa numfashin Ubangiji zai tafi tare da shi.20“Mai fansa zai zo Sihiyona, zuwa waɗanda suke cikin Yaƙub da suka tuba daga zunubansu,” in ji Ubangiji.21“Game da ni dai, ga alkawarina da su,” in ji Ubangiji. “Ruhuna, wanda yake a kanka, da kuma maganata da na sa a bakinka ba za tă rabu da bakinka ba, ko daga bakunan ’ya’yanka ba, ko kuwa daga bakunan zuriyarsu ba daga wannan lokaci zuwa gaba da kuma har abada,” in ji Ubangiji.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Ishaya 59 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/isaiah/059.mp3 66 59