× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Ishaya FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 65 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738394041424344454647484950515253545556575859606162636465661 1 1 : 1 123456789101112131415161718192021222324251 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Ishaya 65 Adana Bayanan kula 1“Na bayyana kaina ga waɗanda ba su tambaye ni ba; ina samuwa ga waɗanda ba su neme ni ba. Ga al’ummar da ba tă kira bisa sunana ba, Na ce, ‘Ga ni, ga ni.’2Dukan yini ina miƙa hannuwana ga mutane masu tayarwa, waɗanda suna tafiya a hanyoyin da ba su da kyau, suna bin tunaninsu,3mutanen da suna cin gaba da tsokanata a fuskata, suna miƙa hadayu a gonaki suna ƙone turare a bagadan tubali;4suna zama a kaburbura su kwana suna yin asirtattun ayyuka; suna cin naman aladu, tukwanensu kuma sun cika da nama marar tsabta;5suna cewa, ‘Ku tsaya a can; kada ku yi kusa da ni, gama na fi ku tsarki!’ Irin mutanen nan hayaƙi ne a hancina, wuta kuma da take cin gaba da ci dukan yini.6“Ga shi, yana nan a rubuce a gabana cewa ba zan ƙyale ba, zan yi cikakken ramuwa; zan yi ramuwa a cinyoyinsu7saboda zunubanku da kuma zunuban kakanninku,” in ji Ubangiji. “Gama sun ƙone turare a kan duwatsu suka kuma ƙazantar da ni a kan tuddai, zan yi musu awo in zuba a cinyoyinsu cikakken ramuwa saboda ayyukansu na dā.”8Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Kamar sa’ad da ruwan ’ya’yan itace yana samuwa a cikin tarin ’ya’yan inabi mutane kuma su ce, ‘Kada a lalace shi, har yanzu akwai abu mai kyau a ciki,’ haka nan zan yi a madadin bayina; ba zan hallaka su duka ba.9Zan fitar da zuriyar Yaƙub, daga Yahuda kuma waɗanda za su mallaki duwatsuna; zaɓaɓɓun mutanena za su gāje su, a can kuma bayina za su zauna.10Sharon zai zama wurin kiwo don shanu, Kwarin Akor kuma wurin hutun garkuna, domin mutanena da suke nemana.11“Amma game da ku waɗanda kuka yashe Ubangiji kuka manta da dutsena mai tsarki kuwa, ku da kuka shimfiɗa tebur don sa’a kuka kuma cika darunan ruwan inabin da aka dama don Ƙaddara,12zan ƙaddara ku ga kaifin takobi, dukanku kuma za ku sunkuya wa mai yanka; gama na yi kira amma ba ku amsa ba, na yi magana amma ba ku saurara ba. Kuka aikata mugunta a gabana kuka kuma zaɓi abin da ba na jin daɗi.”13Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa, “Bayin za su ci, amma ku za ku ji yunwa; bayina za su sha, amma ku za ku ji ƙishi; bayina za su yi farin ciki amma ku za ku sha kunya.14Bayina za su rera da farin cikin zukatansu, amma ku za ku yi kuka daga wahalar zuciya ku kuma yi kururuwa da karayar zuci.15Za ku bar sunanku ga zaɓaɓɓuna yă zama abin la’antarwa; Ubangiji Mai Iko Duka zai kashe ku, amma ga bayina zai ba su wani suna.16Duk wanda zai roƙi albarka a cikin ƙasar zai yi haka da gaskiyar Allah; wanda zai yi rantsuwa a cikin ƙasar zai rantse da gaskiyar Allah. Gama za a manta da wahalolin baya a kuma ɓoye su daga idanuna.17“Ga shi, na halicci sabuwar sama da kuma sabuwar duniya. Abubuwa na dā za a manta da su, ba kuwa za a ƙara tuna da su ba.18Amma ku yi murna ku kuma yi farin ciki har abada a abin da na halitta, gama zan halicci Urushalima ta zama abin murna mutanenta kuwa abin farin ciki.19Zan yi farin ciki a kan Urushalima in kuma yi murna saboda mutanena; a can ba za a ƙara jin karar makoki da na kuka ba.20“A cikinta ba za a ƙara jin jariri ya rayu na ’yan kwanaki kawai ba, ko kuwa wani tsohon da bai cika kwanakinsa ba; duk wanda ya mutu yana da shekaru ɗari za a ce ya mutu a kurciya ne kawai; duk wanda bai kai ɗari ba za a ɗauka la’antacce ne.21Za su gina gidaje su kuma zauna a cikinsu; za su yi shuki a gonakin inabi su kuma ci ’ya’yansu.22Ba za su ƙara gina gidaje waɗansu kuma su zauna a cikinsu ba, ko su yi shuki waɗansu kuma su ci ba. Gama kamar yadda kwanakin itace suke, haka kwanakin mutanena za su kasance; zaɓaɓɓuna za su daɗe suna jin daɗin ayyukan hannuwansu.23Ba za su yi wahala a banza ba ko su haifi ’ya’yan da aka ƙaddara da rashin sa’a; gama za su zama mutanen da Ubangiji ya yi wa albarka, su da zuriyarsu tare da su.24Kafin su yi kira zan amsa; yayinda suke cikin magana zan ji.25Kyarketai da ’yan raguna za su ci abinci tare, zaki kuma zai ci buɗu kamar yadda shanu suke yi, amma ƙura ce za tă zama abincin maciji. Ba za su ƙara cuci ko su yi ɓarna a kan dukan dutsena mai tsarki ba,” in ji Ubangiji.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Ishaya 65 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/isaiah/065.mp3 66 65