× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Irmiya FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 31 123456789101112131415161718192021222324252627282930313233343536373839404142434445464748495051521 1 1 : 25 123456789101112131415161718192021222324252627282930313233343536373839401 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Irmiya 31 Adana Bayanan kula 1“A lokacin nan, zan zama Allah na dukan kabilan Isra’ila, za su kuma zama mutanena,” in ji Ubangiji.2Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Mutanen da suka tsere wa takobi za su sami tagomashi a hamada; zan zo don in ba da hutu ga Isra’ila.”3Ubangiji ya bayyana mana a dā, yana cewa, “Na ƙaunace ku da madawwamiyar ƙauna; na janye ku da ƙauna marar iyaka.4Zan sāke gina ki za ki kuwa sāke ginuwa, ya Budurwar Isra’ila. Za ki kuma ɗauki ganganki ki fita don ki yi rawa da masu farin ciki.5Za ki sāke dasa gonakin inabi a kan tussan Samariya; manoma za su yi shuka a kansu su kuma ji daɗin amfaninsu.6Za a yi ranar da matsara za su tā da murya a kan tuddan Efraim su ce, ‘Ku zo, bari mu haura Sihiyona, zuwa wurin Ubangiji Allahnmu.’ ”7Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Ku rera don farin ciki wa Yaƙub; ku yi sowa don al’ummai da suke nesa. Ka sa a ji yabanku, ku kuma ce, ‘Ya Ubangiji ka ceci mutanenka, raguwar Isra’ila.’8Ga shi, zan kawo su daga ƙasar arewa in tattara su daga iyakar duniya. A cikinsu makafi da guragu za su kasance, mata masu ciki da matan da suke naƙuda; jama’a mai yawan gaske za su komo.9Za su zo da kuka; za su yi addu’a yayinda nake komo da su. Zan bishe su kusa da rafuffukan ruwa a miƙaƙƙiyar hanya inda ba za su yi tuntuɓe ba, domin ni ne mahaifin Isra’ila, Efraim kuma ɗan farina ne.10“Ku ji maganar Ubangiji, ya al’ummai; ku yi shelarta a gaban teku masu nesa cewa, ‘Shi wanda ya watsar da Isra’ila zai tattara su zai kuma lura da garkensa kamar makiyayi.’11Gama Ubangiji zai fanshi Yaƙub zai cece su daga hannun waɗanda suka fi su ƙarfi.12Za su zo su yi sowa don farin ciki a ƙwanƙolin Sihiyona; za su yi farin ciki cikin yalwar Ubangiji hatsi, sabon ruwan inabi da mai, ’ya’yan garken tumaki da na shanu. Za su zama kamar gonar da aka yi wa banruwa, ba za su ƙara yin baƙin ciki ba.13’Yan mata za su yi rawa su kuma yi murna, haka ma samari da tsofaffi. Zan mai da makokinsu farin ciki; zan ta’azantar da su in kuma sa su yi farin ciki a maimakon baƙin ciki.14Zan ƙosar da firistoci da yalwa, mutanena kuma za su cika da yalwa,” in ji Ubangiji.15Ga abin da Ubangiji yana cewa, “An ji murya daga Rama, makoki da kuka mai zafi, Rahila tana kuka domin ’ya’yanta ta kuma ƙi a ta’azantar da ita domin ’ya’yanta ba su.”16Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Hana muryarki kuka da kuma idanunki hawaye, gama za a sāka wa aikinki,” in ji Ubangiji. “Za su komo daga ƙasar abokin gāba.17Saboda haka akwai sa zuciya domin nan gaba,” in ji Ubangiji. “’Ya’yanki za su komo ƙasarsu.18“Tabbatacce na ji gurnanin Efraim yana cewa, ‘Ka hore ni kamar ɗan maraƙi mai ƙin ji, na kuwa horu. Ka mayar da ni, zan kuwa dawo, domin kai ne Ubangiji Allahna.19Bayan na kauce, sai na tuba; bayan na gane, sai na sunkuyar da kaina. Na ji kunya da ƙasƙanci domin ina ɗauke da kunyar ƙuruciyata.’20Efraim ba ƙaunataccen ɗana ba ne, ɗan da nake jin daɗinsa? Ko da yake sau da dama ina maganar gāba a kansa, duk da haka nakan tuna da shi. Saboda haka zuciyata tana marmarinsa; ina da jinƙai mai girma dominsa,” in ji Ubangiji.21“Ki kafa alamun hanya; ki sa shaidun bishewa. Ki lura da babbar hanya da kyau, hanyar da kika bi. Ki komo, ya Budurwar Isra’ila, ki komo zuwa garuruwanki.22Har yaushe za ki yi ta yawo, Ya ’ya marar aminci? Ubangiji zai ƙirƙiro sabon abu a duniya mace za tă kewaye namiji.”23Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila yana cewa, “Sa’ad da na komo da su daga bauta mutane a ƙasar Yahuda da cikin garuruwanta za su sāke yi amfani da waɗannan kalmomi. ‘ Ubangiji ya albarkace ka, ya mazauni mai adalci, ya tsarkakan dutse.’24Mutane za su zauna tare a Yahuda da dukan garuruwansa, manoma da waɗanda suke yawo da garkunansu.25Zan wartsake waɗanda suka gaji in kuma ƙosar da waɗanda ransu ya yi yaushi.”26A kan wannan na farka na duba kewaye. Barcina ya yi mini daɗi.27“Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan kafa gidan Isra’ila da gidan Yahuda da ’ya’yan mutane da na dabbobi.28Kamar yadda na lura da su don su tumɓuke su kuma rusar, su lalatar, su hallaka su kuma kawo masifa, haka zan lura da su don su gina su kuma dasa,” in ji Ubangiji.29“A waɗannan kwanaki mutane ba za su ƙara ce, “ ‘Ubanni suka ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoran ’ya’ya suka mutu ba.’30A maimako, kowa zai mutu saboda zunubinsa; duk wanda ya ci ’ya’yan inabi masu tsami, haƙoransa ne za su mutu.31“Lokaci yana zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan yi sabon alkawari da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.32Ba zai zama kamar alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu ba sa’ad da na kama su da hannu na bishe su daga Masar, domin sun take alkawarina, ko da yake na zama miji a gare su,” in ji Ubangiji.33“Ga alkawarin da zan yi da gidan Isra’ila bayan wannan lokaci,” in ji Ubangiji. “Zan sa dokata a tunaninsu in kuma rubuta ta a zukatansu. Zan zama Allahnsu, za su kuma zama mutanena.34Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabci ba, ko ya koya wa ɗan’uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji,’ domin duk za su san ni, daga ƙaraminsu har zuwa babba,” in ji Ubangiji. “Gama zan gafarta muguntarsu ba zan kuwa ƙara tuna da zunubansu ba.”35Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya kafa rana don tă yi haske a yini shi da ya sa wata da taurari su yi haske da dare, shi da yake dama teku don raƙuman ruwansa su yi ruri Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.36“In dai wannan kafaffiyar ƙa’ida ta daina aiki a gabana,” in ji Ubangiji, “to, sai zuriyar Isra’ila ta daina zama al’umma a gabana.”37Ga abin da Ubangiji yana cewa, “In a iya auna sammai a kuma bincike tushen duniya a ƙarƙas to, sai in ƙi dukan zuriyar Isra’ila ke nan saboda dukan abin da suka yi,” in ji Ubangiji.38“Kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da za a sāke gina wannan birni domina daga Hasumiyar Hananel zuwa Ƙofar Kusurwa.39Ma’auni zai miƙe daga can ya nausa kai tsaye zuwa tudun Gareb sa’an nan ya juya zuwa Gowa.40Dukan kwarin da ake zubar da toka da kuma gawawwaki, da dukan lambatun da suke can har zuwa Kwarin Kidron a gabas zuwa kusurwar Ƙofar Doki, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke birnin ko a rushe shi ba.”Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Irmiya 31 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/jeremiah/031.mp3 52 31