× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Yowel FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 1 1231 1 1 : 1 12345678910111213141516171819201 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Yowel 1 Adana Bayanan kula 1Maganar Ubangiji wadda ta zo wurin Yowel ɗan Fetuwel.2Ku ji wannan, ku dattawa, ku kasa kunne, dukan waɗanda suke zaune a ƙasar. Ko wani abu makamancin haka ya taɓa faruwa a kwanakinku ko a kwanakin kakanninku?3Ku faɗa wa ’ya’yanku, bari kuma ’ya’yanku su faɗa wa ’ya’yansu, ’ya’yansu kuma su faɗa wa tsara ta gaba.4Abin da ɗango ya bari fāri masu girma sun cinye; abin da fāri masu girma suka bari, burduduwa ta cinye; abin da burduduwa ta bari sauran kwari sun cinye.5Ku farka, ku bugaggu, ku yi kuka! Ku yi kuka da ƙarfi, ku dukan mashayan ruwan inabi; ku yi kuka mai ƙarfi saboda sabon ruwan inabi, gama an riga an ƙwace ta daga leɓunanku.6Wata al’umma ta mamaye ƙasata, tana da ƙarfi ba ta kuma ƙidayuwa; tana da haƙoran zaki, da zagar zakanya.7Ta mayar da kuringar inabina kango ta kuma lalatar da itatuwan ɓaurena. Ta ɓamɓare bayansu duka ta kuma jefar da su ta bar rassansu fari fat.8Ku yi makoki kamar budurwa a cikin tsummoki tana baƙin ciki domin mijinta na ƙuruciyarta.9Hadayun hatsi da hadayun sha an yanke su daga gidan Ubangiji. Firistoci suna makoki, su waɗanda suke yi wa Ubangiji hidima.10Filaye sun zama marasa amfani, ƙasa ta bushe; an lalatar da hatsi, sabon ruwan inabin ya bushe, mai kuma ba amfani.11Ku fid da zuciya, ku manoma, ku yi ihu, ku masu noma inabi; ku yi baƙin ciki saboda alkama da sha’ir, saboda an lalata girbin filaye.12Kuringar inabin ta bushe itacen ɓaure kuma ya yi yaushi, ’ya’yan rumman, itacen dabino da itacen gawasa, dukan itatuwan filaye, sun bushe. Tabbatacce farin cikin ’yan adam ya bushe.13Ku sa tsummoki, ya firistoci, ku yi makoki; ku yi ihu, ku da kuke yin hidima a gaban bagade. Zo, ku kwana saye da tsummoki, ku waɗanda kuke yi wa Allahna hidima, gama an yanke hadayun hatsi da hadayun sha daga gidan Allahnku.14Ku yi shelar azumi mai tsarki; ku kira tsarkakan taro. Ku kira dattawa da kuma dukan mazaunan ƙasar zuwa gidan Ubangiji Allahnku, ku kuma yi kuka ga Ubangiji.15Kaito saboda wannan rana! Gama ranar Ubangiji ta kusa, za tă zo kamar hallaka daga wurin Maɗaukaki.16Ba a yanke abinci a idanunmu, farin ciki da kuma murna daga gidan Allahnmu ba?17Iri suna ta yanƙwanewa a busasshiyar ƙasa Ɗakunan ajiya sun lalace, an rurrushe rumbunan hatsin, gama hatsi ya ƙare.18Ji yadda dabbobi suke nishi! Garkunan shanu sun ruɗe saboda ba su da ciyawa, har garkunan tumaki ma suna shan wahala.19A gare ka, ya Ubangiji, nake kira, gama wuta ta cinye wurin kiwo harshen wuta kuma ya ƙone dukan itatuwan jeji.20Har ma namun jeji suna haki gare ka; rafuffuka sun bushe wuta kuma ta cinye wurin kiwo a jeji.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Yowel 1 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/joel/001.mp3 3 1