× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Amos FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 5 1234567891 1 1 : 14 1234567891011121314151617181920212223242526271 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Amos 5 Adana Bayanan kula 1Ku ji wannan magana, ya gidan Isra’ila, ina makokin nan dominku.2“Budurwa Isra’ila ta fāɗi, ba za tă ƙara tashi ba, an yashe ta a ƙasarta, ba wanda zai ɗaga ta.”3Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce, “Birnin da ta fitar da masu ƙarfi dubbai don Isra’ila guda ɗari kaɗai za su dawo; garin da ya fitar da masu ƙarfi ɗari kuwa goma kaɗai za su dawo.”4Ga abin da Ubangiji ya ce wa gidan Isra’ila. “Ku neme ni ku rayu;5kada ku nemi Betel, kada ku je Gilgal, kada ku yi tafiya zuwa Beyersheba. Gama ba shakka Gilgal za tă tafi bauta, za a kuwa mai da Betel ba kome ba.”6Ku nemi Ubangiji ku kuma rayu, ko kuwa zai ratsa yă share gidan Yusuf kamar wuta; zai cinye Betel kuwa ba zai sami wanda zai kashe ta ba.7Ku ne masu mai da gaskiya ta koma ɗaci ku kuma zubar da adalci.8(Shi wanda ya yi Taurarin nan da ake ce Kaza da ’Ya’yanta da kuma Mai Farauta da Kare, wanda ya mai da duhu ya zama haske ya kuma baƙanta rana ta zama dare, yakan kwashe ruwan teku ya zubar a ƙasa, Ubangiji ne sunansa,9yakan kawo hallaka a mafaka mai ƙarfi yakan kuma mai da birnin mai katanga ya zama kufai).10Ba ku son mai yin gaskiya a ɗakin shari’a kuna ƙin mai faɗar gaskiya.11Kuna matsa wa matalauta kuna sa su dole su ba ku hatsi. Saboda haka, ko da yake kun gina gidajen duwatsu, ba za ku zauna a cikinsu ba; ko da yake kun nome gonaki masu kyau, ba za ku sha ruwan inabinsu ba.12Gama na san yawan laifofinku da kuma girman zunubanku. Kuna danne masu adalci kuna kuma cin hanci kuna kuma hana a yi wa matalauta shari’ar adalci a majalisa.13Saboda haka mai hankali yakan yi shiru a lokuta kamar haka, gama lokutan mugaye ne.14Ku yi nagarta, ba mugunta ba; don ku rayu sa’an nan Ubangiji Allah Maɗaukaki zai kasance da ku, kamar yadda kuka ce zai yi.15Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci nagarta; ku dinga yin shari’ar gaskiya a ɗakunan shari’a. Mai yiwuwa Ubangiji Allah Maɗaukaki zai ji tausayin raguwar Yusuf.16Saboda haka ga abin da Ubangiji, Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa, “Za a yi kururuwa a dukan tituna a kuma yi kuka don azaba a dukan wuraren da jama’a sukan taru. Za a yi kira ga manoma su yi kuka masu makoki kuma su yi kuka.17Za a yi kuka a dukan gonakin inabi, gama zan ratsa a cikinku,” in ji Ubangiji.18Kaitonku masu son ganin ranar Ubangiji! Don me kuke son ganin ranar Ubangiji? Za a duhunta ranan nan, ba haske ba.19Za ku zama kamar mutanen da suka guje wa zaki sai suka fāɗa a hannun beyar, ko kuma kamar wanda ya shiga gida ya dāfa hannu a bango sai maciji ya sare shi.20Ashe, ranar Ubangiji ba duhu ba ce, a maimakon haske, duhu wuluk, ba tare da ko ɗan haske ba.21“Na ƙi, ina kuma ƙyamar bukukkuwanku na addini; ba na son ganin tarurrukanku.22Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi, ba zan karɓa ba. Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta, ba zan ɗauke su a bakin kome ba.23Ku tashi daga nan da surutan waƙoƙinku! Ba zan saurari kaɗe-kaɗe da bushe bushenku ba.24Amma bari gaskiya ta kwararo kamar kogi, adalci kuma kamar rafin da ba ya taɓa bushewa!25“Kun kawo mini hadayu da sadakoki shekaru arba’in a cikin jeji, ya ku gidan Isra’ila?26Kun ɗaga masujadar sarkinku, siffofin gumakanku, tauraron allahnku, wanda kuka yi wa kanku.27Saboda haka zan tura ku zaman bauta gaba da Damaskus,” in ji Ubangiji, wanda sunansa ne Allah Mai Iko.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Amos 5 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/amos/005.mp3 9 5