× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Zefaniya FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 1 1231 1 1 : 1 1234567891011121314151617181 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Zefaniya 1 Adana Bayanan kula 1Maganar Ubangiji da ta zo wa Zefaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda.2“Zan hallaka kome a fuskar duniya,” in ji Ubangiji.3“Zan hallaka mutane da dabbobi; zan kuma hallaka tsuntsayen sama da kifayen teku, da gumakan da suke sa mugaye su yi tuntuɓe.” “Sa’ad da zan kawar da mutum daga fuskar duniya,” in ji Ubangiji.4“Zan miƙa hannuna gāba da Yahuda da kuma dukan mazaunan Urushalima. Zan datse raguwar Ba’al daga wannan wuri, da sunayen firistocin gumaka da na marasa sanin Allah,5waɗanda suka rusuna a kan rufin ɗaki don su yi sujada ga rundunar taurari. Waɗanda suka rusuna suka kuma yi rantsuwa da sunan Ubangiji suke kuma rantsuwa da sunan Molek.6Waɗanda suka juya daga bin Ubangiji, ba sa kuma neman Ubangiji ko su nemi nufinsa.”7Ku yi shiru a gaban Ubangiji Mai Iko Duka, gama ranar Ubangiji ta yi kusa. Ubangiji ya shirya hadaya; ya kuma tsarkake waɗanda ya gayyato.8“A ranar hadayar Ubangiji zan hukunta sarakuna da kuma ’ya’yan sarakuna da duk waɗanda suke sanye da rigunan ƙasashen waje.9A wannan rana zan hukunta dukan waɗanda suke kauce taka madogarar ƙofa, waɗanda suke cika haikalin allolinsu da rikici da ruɗu.10“A wannan rana,” in ji Ubangiji, “Za a ji kuka daga Ƙofar Kifi, kururuwa daga Sabon Mazauni, da kuma amo mai ƙarfi daga tuddai.11Ku yi kururuwa, ku da kuke zaune a yankin kasuwa; za a hallaka dukan ’yan kasuwanku, dukan waɗanda suke kasuwanci da azurfa za su lalace.12A wannan lokaci zan bincike Urushalima da fitilu in kuma hukunta waɗanda ba su kula ba, waɗanda suke kamar ruwan inabin da aka bar a ƙasan tukunya, waɗanda suke tsammani, ‘ Ubangiji ba zai yi kome ba nagari ko mummuna.’13Za a washe dukiyarsu, a rurrushe gidajensu. Za su gina gidaje amma ba za su zauna a ciki ba; za su shuka inabi amma ba za su sha ruwansa ba.”14Babbar ranar Ubangiji ta yi kusa, ta yi kusa kuma tana zuwa da sauri. Ku saurara! Kukan ranar Ubangiji za tă yi zafi, za a ji kururuwan jarumi a can.15Ranan nan za tă zama ranar fushi, rana ce ta baƙin ciki da azaba, rana ce ta tashin hankali da lalacewa, ranar duhu baƙi ƙirin, ranar gizagizai da baƙin duhu,16rana ce ta busa ƙaho da kururuwar yaƙi gāba da birane masu mafaka, da kuma kusurwar hasumiyoyi.17“Zan kawo baƙin ciki a kan mutane za su kuma yi tafiya kamar makafi, domin sun yi wa Ubangiji zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura kayan cikinsu kuma kamar najasa.18Azurfarsu ko zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba a ranar fushin Ubangiji.” A cikin zafin kishinsa za a hallaka dukan duniya gama zai kawo ƙarshen dukan mazaunan duniya nan da nan.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Zefaniya 1 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/zephaniah/001.mp3 3 1