× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Mattiyu FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 11 123456789101112131415161718192021222324252627281 1 1 : 28 1234567891011121314151617181920212223242526272829301 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Mattiyu 11 Adana Bayanan kula 1Bayan Yesu ya gama yi wa almajiransa sha biyun nan umarni, sai ya yi gaba daga can don yă koyar yă kuma yi wa’azi a garuruwan Galili.2Sa’ad da Yohanna Mai Baftisma ya ji a kurkuku abin da Kiristi yake yi, sai ya aiki almajiransa3su tambaye shi, “Kai ne wanda zai zo, ko kuwa mu sa ido ga wani?”4Yesu ya amsa ya ce, “Ku koma ku gaya wa Yohanna abin da kuka ji, kuka kuma gani.5Makafi suna gani, guragu suna tafiya, ana warkar da waɗanda suke da kuturta, kurame suna ji, ana tā da matattu, ana kuma yi wa matalauta wa’azin labari mai daɗi.6Mai albarka ne mutumin da bai yi tuntuɓe ba saboda ni.”7Sa’ad da almajiran Yohanna suke barin wurin, sai Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yohanna. “Me kuka je kallo a hamada? Ciyawar da iska take kaɗawa ne?8In ba haka ba, to, me kuka je kallo? Mutum mai sanye da riguna masu kyau ne? A’a, masu sa riguna masu kyau, ai, a fadan sarakuna suke.9To, me kuka je kallo ne? Annabi? I, ina gaya muku, ya ma fi annabi.10Wannan shi ne wanda aka rubuta game da shi cewa, “ ‘Zan aiki ɗan saƙona yă sha gabanka, wanda zai shirya hanyarka a gabanka.’11Gaskiya nake gaya muku. A cikin dukan waɗanda mata suka haifa, ba wani da ya taso da ya fi Yohanna Mai Baftisma girma; duk da haka mafi ƙanƙanta a mulkin sama ya fi shi girma.12Tun daga kwanakin Yohanna Mai Baftisma har yă zuwa yanzu, mulkin sama yana sha da ƙyar, fitanannu kuma sun kama mulkin sama sun riƙe gam.13Gama dukan Annabawa da kuma Doka sun yi ta annabci har yă zuwa kan Yohanna.14In kuna niyya ku yarda da wannan, to, shi ne Iliya da dā ma zai zo.15Duk mai kunnen ji, yă ji.16“Da me zan kwatanta wannan zamani? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,17“ ‘Mun yi muku busa, ba ku kuwa yi rawa ba, mun rera waƙar makoki, ba ku kuwa yi makoki ba.’18Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo ba ya ciye-ciye, ba ya shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da aljani.’19Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”20Sai Yesu ya fara yin tir da biranen da aka yi yawancin ayyukansa na banmamaki, don ba su tuba ba.21“Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba sanye da rigar makoki da toka.22Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shari’a, fiye da ku.23Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaga ki sama ne? A’a, za ki gangara zuwa zurfafa ne. Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne a aka yi a Sodom, da tana nan har yă zuwa yau.24Amma ina gaya miki, za a fi jin tausayin Sodom fiye da ke a ranar shari’a.”25A wannan lokaci sai Yesu ya ce, “Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara.26I, Uba, gama wannan shi ne abin da ka ji daɗin yi.27“Dukan kome Ubana ya danƙa mini. Ba wanda ya san Ɗan sai dai Uban, ba kuma wanda ya san Uban, sai dai Ɗan da kuma waɗanda Ɗan ya so yă bayyana musu shi.28“Ku zo gare ni, dukanku da kuka gaji kuke kuma fama da kaya, zan kuwa ba ku hutu.29Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku.30Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne.”Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Mattiyu 11 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/matthew/011.mp3 28 11