× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Yohanna FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 6 1234567891011121314151617181920211 1 1 : 27 12345678910111213141516171819202122232425262728293031323334353637383940414243444546474849505152535455565758596061626364656667686970711 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Yohanna 6 Adana Bayanan kula 1Ɗan lokaci bayan wannan, sai Yesu ya ƙetare zuwa gaɓar mai nesa na Tekun Galili (wato, Tekun Tibariya),2sai taro mai yawa na mutane suka bi shi domin sun ga abubuwan banmamakin da ya yi ga marasa lafiya.3Sa’an nan Yesu ya hau gefen dutse ya zauna tare da almajiransa.4Bikin Ƙetarewan Yahudawa ya yi kusa.5Sa’ad da Yesu ya ɗaga kai ya ga taro mai yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce wa Filibus, “Ina za mu sayi burodi saboda mutanen nan su ci?”6Ya yi wannan tambayar don yă gwada shi ne kawai, gama ya riga ya san abin da zai yi.7Sai Filibus ya amsa ya ce, “Kai, ko albashin wata takwas ba zai iya sayan isashen burodin da kowa zai ɗan samu kaɗan ba!”8Sai wani daga cikin almajiransa Andarawus, ɗan’uwan Bitrus, ya yi magana,9“Ga wani yaro da ƙananan burodin sha’ir guda biyar da ƙananan kifi biyu, amma me wannan zai yi wa yawan mutanen nan.”10Yesu ya ce, “Ku sa mutanen su zauna.” Wurin kuwa akwai ciyawa da sosai, sai maza suka zazzauna, sun kai wajen dubu biyar.11Sa’an nan Yesu ya ɗauki burodin, ya yi godiya, ya kuma rarraba wa waɗanda suke zaune gwargwadon abin da ya ishe su. Haka kuma ya yi da kifin.12Sa’ad da duk suka ci suka ƙoshi, sai ya ce wa almajiransa, “Ku tattara gutsattsarin da suka rage. Kada kome yă lalace.”13Saboda haka suka tattara su suka kuma cika kwanduna goma sha biyu na gutsattsarin burodin sha’ir biyar nan da suka ragu bayan kowa ya ci.14Bayan mutanen suka ga abin banmamakin da Yesu ya yi, sai suka fara cewa, “Lalle, wannan shi ne Annabin nan mai zuwa duniya.”15Da Yesu ya gane suna shirin su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sāke komawa kan dutsen shi kaɗai.16Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara zuwa tafki,17inda suka shiga jirgin ruwa suka tasar wa haye tafkin zuwa Kafarnahum. A lokacin kuwa duhu ya yi, Yesu kuma bai riga ya zo wurinsu ba tukuna.18Iska mai ƙarfi kuwa tana bugowa, ruwaye kuma suka fara hauka.19Bayan sun yi tuƙi wajen mil uku ko uku da rabi, sai suka ga Yesu ya kusato jirgin ruwan, yana takawa a kan ruwan; sai suka tsorata.20Amma ya ce musu, “Ni ne; kada ku ji tsoro.”21Sa’an nan suka yarda suka karɓe shi a cikin jirgin ruwan, nan da nan kuwa jirgin ya kai gaɓar da za su.22Kashegari taron da suka tsaya a wancan ƙetaren tafkin suka lura cewa jirgin ruwa ɗaya ne yake a can dā ma, kuma sun lura cewa Yesu bai shiga ciki tare da almajiransa ba, gama sun tashi su kaɗai.23Sai ga waɗansu jiragen ruwa daga Tibariya suka iso kusa da wurin da mutanen suka ci burodi bayan Ubangiji ya yi godiya.24Da taron suka lura cewa Yesu da almajiransa ba sa can, sai suka shiga jiragen ruwa suka tafi Kafarnahum neman Yesu.25Da suka same shi a wancan ƙetaren tafkin, sai suka tambaye shi suka ce, “Rabbi, yaushe ka kai nan?”26Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, kuna nemana ne ba don kun ga abubuwan banmamaki ba, sai dai domin kun ci burodi kun ƙoshi.27Kada ku yi aiki saboda abincin da yake lalacewa, sai dai saboda abinci mai dawwama har yă zuwa rai madawwami, wanda Ɗan Mutum zai ba ku. A kansa ne Allah Uba ya sa hatimin amincewarsa.”28Sai suka tambaye shi suka ce, “Me za mu yi don mu aikata ayyukan da Allah yake so?”29Yesu ya amsa, “Aikin Allah shi ne, a gaskata da wanda ya aiko.”30Sai suka tambaye shi, “Wace abin banmamaki ce za ka yi don mu gani mu kuwa gaskata ka? Me za ka yi?31Kakannin-kakanninmu sun ci Manna a hamada; kamar yadda yake a rubuce, ‘Ya ba su burodi daga sama su ci.’ ”32Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba Musa ne ya ba ku burodi daga sama ba, sai dai Ubana ne yake ba ku burodi na gaskiya daga sama.33Gama burodin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama, yana kuma ba wa duniya rai.”34Sai suka ce, “Ranka yă daɗe, daga yanzu ka dinga ba mu wannan burodi.”35Sa’an nan Yesu ya furta cewa, “Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.36Amma kamar yadda na faɗa muku, kun gan ni duk da haka ba ku gaskata ba.37Duk waɗanda Uba ya ba ni za su zo wurina, kuma duk wanda ya zo wurina ba zan kore shi ba ko kaɗan.38Gama na sauko daga sama ba don in cika nufin kaina ba sai dai don in cika nufin shi wanda ya aiko ni.39Nufin wanda ya aiko ni kuwa shi ne, kada in yar da ko ɗaya daga cikin duk waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a rana ta ƙarshe.40Gama nufin Ubana shi ne, duk wanda yake duban Ɗan, ya kuma gaskata shi zai sami rai madawwami, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.”41Da jin haka, Yahudawa suka fara gunaguni a kansa, domin ya ce, “Ni ne burodin da ya sauka daga sama.”42Suka ce, “Kai, wannan ba Yesu ba ne, ɗan Yusuf, wanda mahaifinsa da mahaifiyarsa duk mun san su? Yaya yanzu zai ce, ‘Na sauko daga sama?’ ”43Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ku daina gunaguni a junanku.44Ba mai iya zuwa wurina, sai dai in Uban da ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.45A rubuce yake a cikin Annabawa cewa, ‘Allah zai koyar da dukansu.’ Duk wanda ya saurari Uba, ya kuma koyi daga wurinsa, zai zo wurina.46Ba wanda ya taɓa ganin Uban, sai shi wanda ya zo daga Allah; shi ne kaɗai ya taɓa ganin Uban.47Gaskiya nake gaya muku, wanda ya gaskata yana da rai madawwami.48Ni ne burodin rai.49Kakannin-kakanninku sun ci Manna a hamada, duk da haka suka mutu.50Amma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba.51Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.”52Sai Yahudawa suka fara gardama mai tsanani a junansu suna cewa, “Yaya wannan mutum zai ba mu naman jikinsa mu ci?”53Sai Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, sai kun ci naman jikin Ɗan Mutum kuka kuma sha jininsa, ba za ku kasance da rai a cikinku ba.54Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana da rai madawwami. Ni kuwa zan tashe shi a rana ta ƙarshe.55Gama naman jikina abinci ne na gaskiya jinina kuma abin sha ne na gaskiya.56Duk wanda ya ci naman jikina ya kuma sha jinina, yana cikina, ni kuma ina cikinsa.57Kamar dai yadda Uba mai rai ya aiko ni, ina kuma rayuwa ta saboda shi, haka ma wanda yake ni ne abincinsa zai rayu saboda ni.58Wannan shi ne burodin da ya sauko daga sama. Kakannin-kakanninku sun ci Manna suka kuma mutu, amma duk wanda yake cin wannan burodi zai rayu har abada.”59Ya faɗi wannan ne lokacin da yake koyarwa a cikin majami’a a Kafarnahum.60Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan koyarwa tana da wuya. Wa zai iya yarda da ita?”61Da yake ya san almajiransa suna gunaguni game da wannan, sai Yesu ya ce musu, “Wannan ya ɓata muku rai ne?62Me za ku ce ke nan, in kuka gan Ɗan Mutum yana hawa zuwa inda yake dā!63Ruhu ne yake ba da rai; jikin kam, ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku, Ruhu ne, da kuma rai.64Duk da haka akwai waɗansunku da ba su gaskata ba.” Gama Yesu ya sani tun farko, waɗanda ba su gaskata ba, da kuma wanda zai bashe shi.65Ya ci gaba da cewa, “Shi ya sa na faɗa muku cewa ba mai iya zuwa wurina, sai dai Uba ya yardar masa.”66Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina bin sa.67Sai Yesu ya tambayi Sha Biyun, “Ku ma za ku tafi ne?”68Sai Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Ubangiji wajen wa za mu tafi? Kai ne da kalmomin rai madawwami.69Mun gaskata mun kuma san cewa kai ne Mai Tsarkin nan na Allah.”70Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ba ni na zaɓe ku Sha Biyu ba? Amma ɗayanku Iblis ne!”71(Yana nufin Yahuda, ɗan Siman Iskariyot, wanda, ko da yake ɗaya ne cikin Sha Biyun, zai bashe shi daga baya.)Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Yohanna 6 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/john/006.mp3 21 6