× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Ayyukan Manzanni FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 1 123456789101112131415161718192021222324252627281 1 1 : 1 12345678910111213141516171819202122232425261 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Ayyukan Manzanni 1 Adana Bayanan kula 1A littafina na farko, Tiyofilus, na rubuta game da dukan abin da Yesu ya fara yi, da abin da ya koyar2har zuwa ranar da aka ɗauke shi zuwa sama, bayan ya ba da umarnai ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa.3Bayan wahalarsa, ya bayyana kansa ga waɗannan mutane ya kuma ba da tabbatattun alamu masu yawa cewa yana da rai. Ya bayyana a gare su har kwana arba’in ya kuma yi musu magana game da mulkin Allah.4A wani lokaci, yayinda yake ci tare da su, ya ba su wannan umarni, “Kada ku bar Urushalima, amma ku jira kyautar da Ubana ya yi alkawari, wadda kuka ji na yi magana a kai.5Gama Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma a cikin ’yan kwanaki za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.”6Saboda haka, sa’ad da suka taru, sai suka tambaye shi, “Ubangiji, a wannan lokaci za ka mayar da mulki ga Isra’ila?”7Ya ce musu, “Ba naku ba ne ku san lokuta ko ranakun da Uban ya shirya cikin ikonsa.8Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.”9Bayan ya faɗi wannan, sai aka ɗauke shi sama a idanunsu sai wani girgije ya rufe shi daga ganinsu.10Suna zuba ido a bisa, zuwa cikin sararin sama yayinda yake tafiya, nan da nan, sai ga mutane biyu saye da fararen riguna tsaye kusa da su.11Sai suka ce, “Mutanen Galili, don me kuke tsaye a nan kuna duban sararin sama? Wannan Yesu, wanda aka ɗauke daga gare ku zuwa sama, zai komo daidai yadda kuka ga ya tafi sama.”12Sai suka koma Urushalima daga tudun da ake kira Dutsen Zaitun, tafiyar ranar Asabbaci guda daga birnin.13Da suka iso, sai suka hau gidan sama, zuwa ɗakin da suke zama. Waɗanda suka kasance kuwa su ne, Bitrus, Yohanna, Yaƙub da Andarawus; Filibus da Toma; Bartolomeyu da Mattiyu; Yaƙub ɗan Alfayus da Siman Zilot, da kuma Yahuda ɗan Yaƙub.14Waɗannan duka suka duƙufa cikin addu’a, tare da waɗansu mata da Maryamu mahaifiyar Yesu, da kuma tare da ’yan’uwansa.15A waɗancan kwanakin Bitrus ya miƙe tsaye cikin ’yan’uwa masu bi (taron da ya yi kusan mutum ɗari da ashirin)16ya ce, “’Yan’uwana, dole a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya yi magana tun da daɗewa ta bakin Dawuda game da Yahuda, wanda ya zama jagora ga waɗanda suka kama Yesu17dā shi ɗaya ne cikinmu, ya kuma yi hidima a cikin aikin nan.”18(Da ladar da ya samu saboda muguntarsa Yahuda ya sayi wani fili; a can ya fāɗi da kā, jikinsa ya fashe, hanjinsa kuma duk suka zubo.19Kowa a Urushalima ya ji game da wannan, saboda haka suka kira wannan filin Akeldama, da yarensu, wato, Filin Jini.)20Bitrus ya ce, “Gama yana a rubuce a cikin Littafin Zabura cewa, “ ‘Bari wurinsa yă zama babu kowa; kada kowa ya zauna a cikinsa,’ kuma, “ ‘Bari wani ya ɗauki matsayinsa na shugabanci.’21Saboda haka dole a zaɓi ɗaya daga cikin mutanen da suke tare da mu duk lokacin da Ubangiji Yesu yake shiga da fita a cikinmu,22farawa daga baftisma ta Yohanna har zuwa sa’ad da aka ɗauke Yesu daga gare mu. Gama dole ɗaya daga waɗannan ya zama shaidar tashinsa daga matattu tare da mu.”23Saboda haka suka gabatar da mutane biyu. Yusuf mai suna Barsabbas (da aka kuma sani da Yustus) da kuma Mattiyas.24Sai suka yi addu’a suka ce, “Ubangiji, ka san zuciyar kowa. Nuna mana wanne a cikin waɗannan biyu da ka zaɓa25ya karɓi wannan aikin manzanci, wanda Yahuda ya bari don yă tafi wurin da yake nasa.”26Sa’an nan suka jefa ƙuri’u, ƙuri’ar kuwa ta fāɗo a kan Mattiyas; sai aka sa shi cikin manzannin nan goma sha ɗaya.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Ayyukan Manzanni 1 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/acts/001.mp3 28 1