× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Galatiyawa FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 4 1234561 1 1 : 4 123456789101112131415161718192021222324252627282930311 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Galatiyawa 4 Adana Bayanan kula 1Abin da nake nufi shi ne, muddin magāji yana ɗan yaro ne tukuna, babu bambanci tsakaninsa da bawa, ko da yake shi ne da mallakar kome.2Yana ƙarƙashin iyayen goyonsa da masu riƙon amana har yă zuwa cikar lokacin da mahaifinsa ya sa.3Haka yake, sa’ad da muke ’yan yara, mun kasance cikin bauta a ƙarƙashin ƙa’idodin duniya.4Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka,5domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya.6Da yake ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “ Abba, Uba.”7Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.8Dā da ba ku san Allah ba, ku bayi ne ga waɗanda a ainihi ba alloli ba ne.9Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma a ce Allah ya san ku, yaya kuke sāke komawa ga ƙa’idodin duniya marasa ƙarfi, abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu ne?10Kuna kiyaye ranaku da watanni da lokuta da shekaru na musamman!11Kai, kun ba ni tsoro, don ya zama kamar duk wahalar da na yi a kanku banza ne!12Ina roƙonku ’yan’uwa, ku zama kamar ni, gama na zama kamar ku. Ba ku yi mini wani laifi ba.13Kun san rashin lafiyar da na yi, shi ne ya yi mini hanyar da na kawo muku bishara da farko.14Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce mala’ikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa.15Me ya faru da dukan farin cikinku? Na tabbata, a lokacin, da mai yiwuwa ne da kun ciccire idanunku kun ba ni.16Yanzu na zama abokin gābanku don na faɗa muku gaskiya ke nan?17Waɗancan mutane suna neman su rinjaye ku da ƙwazo, amma ba da kyakkyawar aniya ba. Abin da suke so shi ne su raba ku da mu, saboda ƙwazonku yă koma gare su.18Yana da kyau ku kasance da irin wannan niyya idan da nufi mai kyau ne, ku kuma kasance a haka koyaushe ba sai ina tare da ku ba.19Ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har sai Kiristi ya kahu a cikinku.20Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canja muryata mana! Gama na damu ƙwarai saboda ku!21Ku gaya mini, ku da kuke so ku zauna a ƙarƙashin Doka, ba ku san abin da Doka ta ce ba ne?22Gama a rubuce yake cewa Ibrahim yana da ’ya’ya biyu maza, ɗaya ta wurin mace ’yar aikin gidansa, ɗaya kuma ta wurin ainihin matarsa.23Ɗansa na wajen mace ’yar aikin gidansa ya zo bisa ga ƙa’idar jiki ne; amma ɗansa na wajen ainihin matarsa ya zo a sakamakon alkawarin ne.24Za a iya ɗaukan waɗannan al’amura a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawura biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar ’ya’yan da za su zama bayi. Hagar ke nan.25Hagar tana a matsayin Dutsen Sinai a Arabiya tana kuma kwatancin birnin Urushalima na yanzu, gama ita baiwa ce tare da ’ya’yanta.26Amma Urushalimar da take sama ’yantacciya ce, ita ce kuma mahaifiyarmu.27Gama a rubuce yake cewa, “Ki yi farin ciki, ya ke bakararriya, wadda ba ta haihuwa ki ɓarke da murna, ki kuma tā da murya, ke da ba kya naƙuda; domin da yawa ne ’ya’yan macen da aka yashe, fiye da na mai miji.”28To, ku ’yan’uwa, ku ’ya’yan alkawari ne kamar Ishaku.29A wancan lokaci, wannan ɗa wanda aka haifa ta wurin ƙa’idar jiki ya tsananta wa wanda aka haifa ta ikon Ruhu. Haka ma yake har yanzu.30Amma me Nassi ya ce? Nassi ya ce, “Kori macen nan ’yar aikin gida da ɗanta don ɗan mace ’yar aikin gida ba zai taɓa raba gādo tare da ɗa na ainihin matarka ba.”31Saboda haka, ’yan’uwa, mu ba ’ya’yan mace ’yar aikin gida ba ne, amma na ainihin matan gidan ne.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Galatiyawa 4 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/galatians/004.mp3 6 4