× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Maimaitawar Shariʼa FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 1 123456789101112131415161718192021222324252627282930313233341 1 1 : 1 123456789101112131415161718192021222324252627282930313233343536373839404142434445461 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Maimaitawar Shariʼa 1 Adana Bayanan kula 1Waɗannan su ne kalmomin da Musa ya yi wa dukan Isra’ila, a hamada gabas da Urdun, wato, Araba, ɗaura da Suf, tsakanin Faran da Tofel, Laban, Hazerot da Dizahab.2(Yakan ɗauki kwana goma sha ɗaya daga Horeb zuwa Kadesh Barneya ta hanyar Dutsen Seyir.)3A shekara ta arba’in, a rana ta fari ga wata na goma sha ɗaya, Musa ya yi shela ga Isra’ilawa game da dukan abin da Ubangiji ya umarta shi game da su.4Wannan ya faru bayan ya ci Sihon sarkin Amoriyawa wanda ya yi mulki a Heshbon da yaƙi. A Edireyi kuma ya ci Og sarkin Bashan wanda ya yi mulki a Ashtarot da yaƙi.5Gabas da iyakar Mowab, Musa ya fara bayyana wannan doka, yana cewa,6Ubangiji Allahnmu ya faɗa mana a Horeb cewa, “Daɗewarku a wannan dutse ya isa haka.7Ku tashi, ku ci gaba zuwa ƙasar tudun Amoriyawa; ku tafi wurin dukan maƙwabta a cikin Araba, a cikin duwatsu, a gindin yammancin tuddai, a Negeb da kuma a ta kwaruruka, da ƙasar Kan’aniyawa da kuma zuwa Lebanon, har zuwa babban kogi, wato, Yuferites.8Duba na riga na ba ku wannan ƙasa. Ku shiga ku mallaki ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba wa kakanninku, ga Ibrahim, Ishaku da kuma Yaƙub, da kuma ga zuriyarsu bayansu.”9A wancan lokaci na faɗa muku cewa, “Ku kaya ne masu nauyi da ni kaɗai ba zan iya ɗauka ba.10Ubangiji Allahnku ya ƙara yawanku har yau kuka zama da yawa kamar taurari a sarari.11Bari Ubangiji, Allahn kakanninku yă ƙara yawanku sau dubu, yă kuma albarkace ku yadda ya yi alkawari!12Amma yaya zan ɗauka dukan damuwoyinku da nawayarku da kuma faɗace-faɗacenku duka ni kaɗai?13Ku zaɓi waɗansu masu hikima, masu ganewa, da kuma mutanen da ake girmama daga kowace kabilarku, zan kuma sa su a kanku.”14Kuka amsa mini, kuka ce, “Abin da ka ce za ka yi, yana da kyau.”15Saboda haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma’amala da jama’a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu-dubu, waɗansu a kan ɗari-ɗari, waɗansu a kan hamsin-hamsin, waɗansu kuma a kan goma-goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku.16Na kuma umarci alƙalanku a wancan lokaci, na ce, “Ku yi adalci cikin shari’a tsakanin ’yan’uwanku, ko damuwar tana tsakanin ’yan’uwa Isra’ilawa ne, ko kuwa tsakanin Isra’ilawa da baƙin da suke zaune a cikinku.17Kada ku nuna sonkai a cikin hukuncinku, ku saurari kowane ɓangare, babba da ƙarami, kada ku ji tsoron wani, gama hukunci na Allah ne. Ku kawo kowane batun da ya sha ƙarfinku, zan kuwa saurare shi.”18A wancan lokacin kuwa na faɗa muku dukan abin da ya kamata ku yi.19Sa’an nan, muka kama hanya daga Horeb muka ratsa wajen ƙasar tudun Amoriyawa ta dukan hamadarta mai fāɗi, da kuma mai bantsoron da kuka gani, muka kuma kai Kadesh Barneya yadda Ubangiji, Allahnmu ya umarce mu.20Sai na ce muku, “Kun iso ƙasar tudun Amoriyawa, wadda Ubangiji, Allahnmu yake ba mu.21Duba, Ubangiji Allahnku ya ba ku ƙasar. Ku haura ku mallake ta yadda Ubangiji Allahn kakanninku ya faɗa muku. Kada ku ji tsoro, kada ku fid da zuciya.”22Sai dukanku kuka zo wurina kuka ce, “Bari mu aiki mutane su yi gaba su leƙi mana asirin ƙasar, su kuma kawo mana labari game da hanyar da za mu bi, da kuma biranen da za mu shiga.”23Ra’ayin nan naku ya yi mini kyau, saboda haka na zaɓe ku goma sha biyu, mutum guda daga kowace kabila.24Suka tafi, suka haura zuwa ƙasar tudu, suka kai Kwarin Eshkol, suka leƙo asirin ƙasar.25Suka ɗebi ’ya’yan itatuwan ƙasar, suka sauko mana da su, suka kuma ba da labari cewa, “Ƙasar da Ubangiji Allahnmu yake ba mu, kyakkyawa ce.”26Amma ba ku yi niyya ku haura ba, kuka yi tawaye gāba da umarnin Ubangiji Allahnku.27Kuka yi gunaguni a cikin tentunanku, kuna cewa, “ Ubangiji ya ƙi mu; shi ya sa ya fitar da mu daga Masar don yă ba da mu ga hannuwan Amoriyawa su hallaka mu.28Ina za mu? ’Yan’uwanmu suka sa muka fid da zuciya. Suka ce, ‘Mutanen sun fi mu ƙarfi, sun kuma fi mu tsayi; biranen manya ne, da katanga har sama. Mun ma ga Anakawa a can.’ ”29Sai na ce muku, “Kada ku firgita; kada ku ji tsoronsu.30Ubangiji Allahnku yana a gabanku, zai yi yaƙi saboda ku, kamar yadda ya yi a kan idanunku a Masar,31da kuma a cikin hamada. A can ma kun ga yadda Ubangiji Allahnku ya riƙe ku ko’ina da kuka tafi, kamar yadda mahaifi yakan riƙe ɗansa, sai da kuka kai wannan wuri.”32Duk da haka, ba ku amince da Ubangiji Allahnku ba,33shi da ya sha gabanku a tafiyarku, cikin wuta da dad dare da kuma girgije da rana, don yă nemi wurare domin ku kafa sansani, don kuma yă nuna muku hanyar da za ku bi.34Da Ubangiji ya ji abin da kuka faɗa, sai ya husata, ya kuma yi rantsuwa ya ce,35“Babu wani a cikin wannan muguwar tsara da zai ga ƙasa mai kyau da na rantse zan ba wa kakanninku,36sai dai Kaleb ɗan Yefunne. Zai gan ta, zan ba shi duk ƙasar da tafin ƙafarsa ta taka, shi da zuriyarsa, gama ya bi Ubangiji da zuciya ɗaya.”37Saboda ku Ubangiji ya husata da ni, ya kuma ce, “Kai ma, ba za ka shiga ƙasar ba.38Amma mataimakinka, Yoshuwa ɗan Nun, zai shiga. Ka ƙarfafa shi gama shi ne zai jagoranci Isra’ila su gāje ta.39Amma ’ya’yanku ƙanana waɗanda ba su san mugunta ko nagarta ba, waɗanda kuke tsammani za a kwashe su ganima, su za su shiga ƙasar. Zan ba da ita gare su, za su kuwa mallake ta.40Amma ku kam, sai ku juya, ku koma cikin hamada ta hanyar Jan Teku.”41Sai kuka amsa, kuka ce, “Mun yi zunubi ga Ubangiji. Za mu haura mu yi yaƙi yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu.” Saboda haka kowannenku ya yi ɗamara da kayan yaƙinsa, kuka yi tsammani zai zama muku da sauƙi ku ci ƙasar tuddai da yaƙi.42Amma Ubangiji ya ce mini, “In faɗa muku, ‘Kada ku fāɗa musu da yaƙi, gama ba zai kasance tare da ku ba. Idan kuka kuskura, abokan gābanku za su murƙushe ku.’ ”43Sai na faɗa muku, amma ba ku saurara ba. Kuka yi tawaye ga umarnin Ubangiji, a cikin jahilcinku kuwa kuka taka, kuka haura cikin ƙasar tudu.44Amoriyawan da suke zama a waɗannan tuddai, suka fito kamar tarin ƙudan zuma gāba da ku, suka kore ku, suka fatattake ku daga Seyir har zuwa Horma.45Kuka dawo, kuka yi kuka a gaban Ubangiji, amma bai kula da ku ba, balle yă saurare ku.46Haka kuwa kuka zauna a Kadesh kwanaki masu yawa, kuka ci lokaci a can.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Maimaitawar Shariʼa 1 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/deuteronomy/001.mp3 34 1