× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 1 Timoti FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 5 1234561 1 1 : 3 123456789101112131415161718192021222324251 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 1 Timoti 5 Adana Bayanan kula 1Kada ka tsawata wa dattijo, sai dai ka gargaɗe shi a matsayinka. Ka ɗauki samari a matsayin ’yan’uwanka,2tsofaffin mata kuwa sai ka ce uwaye, ’yan mata kuma a matsayin ’yan’uwa da matuƙar tsarki.3Ka girmama gwauraye waɗanda suke cikin bukata ta ainihi.4Amma in gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah.5Gwauruwa wadda ba ta da kowa da zai taimake ta, za tă sa zuciyarta ga Allah, tana roƙo da addu’o’i dare da rana gare shi don taimako.6Amma gwauruwar da take zaman jin daɗi, matacciya ce tun tana da rai.7Ka umarce su game da waɗannan abubuwa, don su kasance marasa abin zargi.8In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.9Kada a lasafta gwauruwa cikin jerin gwauraye sai ta wuce shekara sittin, ta kuma yi zaman aminci ga mijinta,10aka kuma santa sosai saboda ayyuka masu kyau, kamar renon ’ya’ya, da karɓan baƙi, tana yi wa tsarkaka hidima, tana taimakon waɗanda suke cikin wahala tana kuma ba da kanta ga yin kowane aikin mai kyau.11Game da gwauraye masu ƙuruciya kuwa, kada ka sa su cikin wannan lissafi. Gama sa’ad da sha’awar jikinsu ta kāsa daurewa game da wa’adin da suka yi da Kiristi, sai su so yin aure.12Ta haka suna jawo wa kansu hukunci, saboda sun karya alkawarinsu na farko.13Ban da haka, sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida-gida. Ba kawai sun zama masu zaman banza ba, har ma sun zama masu gulma da masu shisshigi, suna faɗin abubuwan da bai kamata su faɗa ba.14Saboda haka ina ba wa gwauraye masu ƙuruciya shawara su yi aure, su sami ’ya’ya, su lura da gidajensu kada kuwa su ba abokin gāba zarafin ɓata suna.15Waɗansu dai sun riga sun bauɗe sun bi Shaiɗan.16In mace mai bi tana da gwauraye a iyalinta, ya kamata tă taimake su, kada tă bar wa ikkilisiya wannan nauyi, domin ikkilisiya ta sami zarafin taimakon gwaurayen da suke da bukata ta ainihi.17Dattawan da suka bi da al’amuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu wa’azi ne da kuma koyarwa.18Gama Nassi ya ce, “Kada ka sa wa bijimi takunkumi yayinda yake sussukar hatsi,” da kuma, “Ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.”19Kada ka saurari ƙara game da dattijo sai da shaidu biyu ko uku.20Amman waɗannan dattawa waɗanda suke yin zunubi kuwa sai ka kwaɓe su a gaban jama’a, don saura su ji tsoro.21Na gama ka da Allah, da Kiristi Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala’iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka nuna bambanci.22Kada ka yi garajen ɗibiya hannuwa, kada kuma ka yi tarayya a cikin zunuban waɗansu. Ka kiyaye kanka da tsarki.23Ka daina shan ruwa kaɗai, yi amfani da ruwan inabi kaɗan saboda cikinka da kuma yawan rashin lafiyarka.24Zunuban waɗansu mutane a fili suke, suna shan gabansu zuwa hukunci; zunuban waɗansu kuwa sukan bi su a baya.25Haka ma ayyuka nagari a fili suke, ko ba ma a fili suke ba, ba a iya ɓoye su.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 1 Timoti 5 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/1timothy/005.mp3 6 5