× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Yaƙub FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 1 123451 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920212223242526271 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Yaƙub 1 Adana Bayanan kula 1Yaƙub, bawan Allah da kuma na Ubangiji Yesu Kiristi, Zuwa ga kabilan nan goma sha biyu, da suke warwartse a cikin al’ummai. Gaisuwa mai yawa.2Ku ɗauki wannan da farin ciki mai tsabta, ’yan’uwana, duk sa’ad da gwaje-gwaje na kowane iri suka zo muku,3domin kun san cewa gwajin bangaskiyarku yakan haifi daurewa.4Dole daurewa ta kammala aikinta don ku zama balagaggu da kuma cikakku, ba ku kuma rasa kome ba.5In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.6Amma sa’ad da ya roƙa, dole yă gaskata, ba tare da shakka ba, domin shi mai shakka, yana kama da raƙumar ruwan tekun da iska take kori tana kuma ɓuɓɓugowa.7Kada irin wannan mutum yă yi tsammani zai sami wani abu daga Ubangiji;8shi mai zuciya biyu ne, marar tsai da zuciyarsa wuri ɗaya a cikin duk abin da yake yi.9Bari ɗan’uwan da yake cikin halin ƙasƙanci yă yi taƙama a matsayinsa na ɗaukaka.10Amma wanda yake mai arziki, ya kamata yă yi taƙama a matsayinsa na ƙasƙanci, gama ba zai daɗe ba kamar furen jeji.11Gama in rana ta fito ta yi zafi mai tsanani sai ta sa tsiro yă yanƙwane tsiro; furensa yă kakkaɓe, kyansa kuma yă lalace. Haka ma mai arziki zai shuɗe yayinda yake cikin harkarsa.12Mai albarka ne mutumin da yake daurewa cikin gwaji, gama bayan ya yi nasara da gwajin, zai sami rawanin rai wanda Allah ya yi alkawari ga waɗanda suke ƙaunarsa.13Sa’ad da aka jarrabci mutum, kada yă ce, “Allah ne yake jarrabtarsa.” Gama ba ya yiwuwa a jarrabci Allah da mugunta, shi kuma ba ya jarrabtar kowa;14amma akan jarrabce kowane mutum sa’ad da muguwar sha’awarsa ta janye shi ta kuma rinjaye shi.15Sa’an nan, bayan da sha’awar ta yi ciki, takan haifi zunubi; zunubi kuwa, sa’ad da ya balaga yakan haifi mutuwa.16Kada a ruɗe ku, ’yan’uwana ƙaunatattu.17Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.18Ya zaɓa yă haife mu ta wurin kalmar gaskiya, domin mu zama ’ya’yan fari na dukan abin da ya halitta.19’Yan’uwana ƙaunatattu, ku lura da wannan. Ya kamata kowa yă kasance mai saurin saurara, ba mai saurin magana ba, ba kuma mai saurin fushi ba,20gama fushin mutum ba ya kawo rayuwar adalcin da Allah yake so.21Saboda haka, ku rabu da ƙazamin hali da kuma kowace irin mugunta ku kuma yi na’am da maganar da aka shuka a cikinku da tawali’u, wadda za tă iya cetonku.22Kada ku zama masu ji kawai, ku ruɗi kanku. A maimakon haka ku zama masu yin abin da ta ce.23Duk wanda yake ji magana ne kawai, bai kuwa aikata abin da ta ce ba, yana kama da mutumin da ya kalli fuskarsa a madubi24bayan ya kalli kansa, sa’ad da ya tashi daga wurin, nan da nan sai yă manta da kamanninsa.25Amma duk mai duba cikakkiyar ƙa’idan nan ta ’yanci, ya kuma nace a kanta, ya zama ba mai ji ne kawai yă mance ba, sai dai mai yi ne yă zartar, to wannan shi za a yi wa albarka a cikin abin da yake yi.26In wani ya ɗauki kansa mai addini ne duk da haka bai ƙame harshensa ba, ruɗin kansa yake yi addininsa kuwa banza ne.27Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Yaƙub 1 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/james/001.mp3 5 1