× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Yoshuwa FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 1 1234567891011121314151617181920212223241 1 1 : 1 1234567891011121314151617181 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Yoshuwa 1 Adana Bayanan kula 1Bayan mutuwar Musa bawan Ubangiji, sai Ubangiji ya ce wa Yoshuwa ɗan Nun, mataimakin Musa,2“Bawana Musa ya mutu. Yanzu sai ka tashi tare da mutanen nan duka, ku yi shirin ƙetare kogin Urdun zuwa cikin ƙasar da zan ba su Isra’ilawa.3Zan ba ku duk ƙasar da za ku taka, kamar yadda na yi wa Musa alkawari.4Ƙasar da ta kama daga hamada zuwa Lebanon, zuwa babban Kogin, wato, Kogin Yuferites, da dukan ƙasar Hittiyawa zuwa Bahar Rum, wajen yamma.5Ba wanda zai yi tsayayya da kai dukan kwanakin ranka. Yadda na kasance tare da Musa, haka zan kasance tare da kai; ba zan taɓa rabuwa da kai ba; ba zan yashe ka ba.6“Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, gama kai za ka bi da mutanen nan har su karɓi ƙasar da na yi wa kakanninsu alkawari zan ba su.7Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro, ka yi lura fa, ka yi biyayya da dokokin da bawana Musa ya ba ka; kada ka kauce ga bin dokokin ko hagu ko dama, domin ka yi nasara a duk, inda za ka je.8Kada ka bar Littafin Dokokin nan yă rabu da bakinka, sai dai ka yi ta tunani game da shi dare da rana, don ka lura, ka yi duk abin da aka rubuta a ciki, ta haka ne za ka yi nasara cikin duk abin da za ka yi.9Ba ni na umarce ka ba? Ka yi ƙarfin hali ka kuma kasance da rashin tsoro. Kada ka ji tsoro; kada ka karaya, gama Ubangiji Allahnka zai kasance tare da kai duk inda za ka je.”10Saboda haka sai Yoshuwa ya umarci shugabannin mutane,11“Ku ratsa cikin sansani, ku gaya wa mutane, ‘Ku shirya guzurinku. Nan da kwana uku za ku ƙetare Urdun a nan, don ku je ka mallaki ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ta zama taku.’ ”12Amma Yoshuwa ya ce wa mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse,13“Ku tuna da umarnin da Musa bawan Ubangiji ya yi muku. ‘ Ubangiji Allahnku ya ba ku hutawa, ya kuma ba ku wannan ƙasa.’14Matanku, da yaranku, da kuma dabbobinku za su kasance a ƙasar da Musa ya ba ku a gabashin Urdun, amma dole mayaƙanku, su yi shirin yaƙi su haye, su yi gaba tare da ’yan’uwanku, za ku taimaki ’yan’uwanku15har sai lokacin da Ubangiji ya ba su hutawa, kamar yadda ya yi muku, kuma har sai su ma sun ƙwace ƙasar da Ubangiji Allahnku ya yi alkawari zai ba su. Bayan haka ne za ku koma ku mallaki ƙasarku, wadda Musa bawan Ubangiji ya ba ku a gabashin Urdun.”16Sai suka amsa wa Yoshuwa suka ce, “Duk abin da ka ce mu yi, za mu yi. Duk inda kuma ka aike mu, za mu je.17Kamar yadda muka yi wa Musa biyayya, haka za mu yi maka biyayya. Ubangiji Allahnka ya kasance tare da Musa.18Duk wanda ya yi wa maganarka tawaye, ya ƙi yă yi biyayya da maganarka, ko da umarnin da ka ba shi, za a kashe shi. Ka dai ƙarfafa ka kuma yi ƙarfi hali!”Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Yoshuwa 1 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/joshua/001.mp3 24 1