× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 1 Bitrus FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 1 123451 1 1 : 1 123456789101112131415161718192021222324251 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 1 Bitrus 1 Adana Bayanan kula 1Bitrus, manzon Yesu Kiristi, Zuwa ga zaɓaɓɓu na Allah, baƙi a duniya, da suke a warwatse ko’ina a Fontus, Galatiya, Kaffadokiya, Asiya da kuma Bitiniya,2waɗanda aka zaɓa bisa ga rigyasanin Allah Uba, ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu, don biyayya ga Yesu Kiristi, su kuma sami yayyafan jininsa. Alheri da salama su zama naku a yalwace.3Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu,4da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku,5ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci.6A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri.7Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi.8Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi,9gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.10Game da ceton nan, annabawa, waɗanda suka yi maganar alherin da za tă zo gare ku, sun yi bincike mai zurfi, a natse,11suna ƙoƙari su san lokaci da kuma yanayin da Ruhun Kiristi da yake cikinsu yana nunawa sa’ad da ya yi faɗi a kan wahalolin Kiristi da kuma ɗaukaka da za tă bi.12Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, sa’ad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku wa’azin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko mala’iku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa.13Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi.14Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci.15Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi;16gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”17Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma.18Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba,19sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani.20An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku.21Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.22Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya.23Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah.24Gama, “Dukan mutane kamar ciyawa suke, darajarsu kuma kamar furannin jeji ne; ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe,25amma maganar Ubangiji tana nan har abada.” Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Sabon Rai Don Kowa 2020 1 Bitrus 1 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/1peter/001.mp3 5 1