× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Yahuda FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 1 11 1 1 : 1 123456789101112131415161718192021222324251 1 1 Yahuda 1 Adana Bayanan kula 1Yahuda, bawan Yesu Kiristi, ɗan’uwan Yaƙub, Zuwa ga waɗanda aka kira, waɗanda Allah Uba yake ƙauna, waɗanda kuma Yesu Kiristi ya kiyaye.2Jinƙai, salama da kuma ƙauna, su kasance tare da ku a yalwace.3Abokaina ƙaunatattu, ko da yake na yi marmari ƙwarai in rubuta muku game da ceton nan namu, sai na ga ya dace in rubuta, in gargaɗe ku ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya wadda aka danƙa wa mutane masu tsarki na Allah sau ɗaya tak.4Na faɗa haka ne domin waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā sun shiga cikinku a ɓoye. Su fa marasa tsoron Allah ne. Su ne waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci, suna kuma mūsun Yesu Kiristi wanda shi ne Makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu.5Ko da yake kun riga kun san duk wannan, ina so in tuna muku cewa Ubangiji ya ceci mutanensa daga Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba.6Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan.7Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta.8Haka yake da masu mafarke-mafarken nan, gama sun ƙazantar da jikunansu, suka ƙi bin masu mulki, suna ɓata sunan talikan sararin sama.9Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!”10Duk da haka mutanen nan suna maganar banza a kan kome da ba su gane ba; kuma abubuwan da suka fahimta bisa ga jiki, kamar dabbobi marasa hankali, waɗannan abubuwa ne suke hallaka su.11Kaitonsu! Gama sun kama hanyar Kayinu; sun ruga a guje garin neman riba cikin kuskure kamar Bala’am; aka kuma hallaka su cikin tawayen Kora.12Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus.13Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada.14Enok ma, wanda yake na bakwai daga Adamu, ya yi annabci game da waɗannan mutane cewa, “Duba, Ubangiji yana zuwa da dubu dubban tsarkakansa15don yă yi wa kowa shari’a, yă kuma hukunta duk marasa tsoron Allah game da dukan ayyukansu na rashin tsoron Allah da suka aikata ta hanyar rashin tsoron Allah, da kuma dukan baƙaƙen kalmomin da masu zunubi marasa tsoron Allah suka faɗa game da shi.”16Waɗannan mutane dai, gunaguni gare su, kullum ganin laifin waɗansu suke yi. Muguwar sha’awa ce kaɗai tunaninsu. Sun cika da banzar magana ta yabon kansu. Suna ruɗin mutane da zaƙin baki don samun ribar kansu.17Amma ku abokaina ƙaunatattu, ku tuna da abin da manzannin Ubangijinmu Yesu Kiristi suka faɗa a dā.18Sun ce muku, “A kwanakin ƙarshe za a kasance da masu ba’a waɗanda za su bi sha’awace-sha’awacensu na rashin tsoron Allah.”19Waɗannan mutanen ne, suke kawo rabe-rabe, masu bin abin da jiki yake so, marasa Ruhu.20Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi addu’a cikin Ruhu Mai Tsarki.21Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yă kawo ku ga rai madawwami.22Ku ji tausayin waɗanda suke shakka;23ku cece waɗansu ta wurin fizge su daga wuta. Ga waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro, har ma ku yi ƙyamar tufafin da suka ɓata da ayyukansu na jiki.24To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki.25Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Yahuda 1 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/jude/001.mp3 1 1