× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Madurese Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 Farawa FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 47 12345678910111213141516171819202122232425262728293031323334353637383940414243444546474849501 1 1 : 1 123456789101112131415161718192021222324252627282930311 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Farawa 47 Adana Bayanan kula 1Yusuf ya tafi yă faɗa wa Fir’auna, “Mahaifina da ’yan’uwana, tare da garkunansu da shanunsu da kome da suke da shi, sun zo daga ƙasar Kan’ana, suna kuwa a Goshen yanzu.”2Sai ya zaɓi mutum biyar daga cikin ’yan’uwansa, ya gabatar da su a gaban Fir’auna.3Fir’auna ya tambayi ’yan’uwan, “Mece ce sana’arku?” Suka amsa wa Fir’auna suka ce, “Bayinka makiyaya ne, kamar yadda kakanninmu suke.”4Suka kuma ce masa, “Mun zo, mu zauna a nan na ɗan lokaci, gama yunwa ta yi tsanani a Kan’ana, dabbobin bayinka kuma ba su da wurin kiwo. Saboda haka yanzu, muna roƙonka, bari bayinka su zauna a Goshen.”5Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Mahaifinka da ’yan’uwanka sun zo maka,6ƙasar Masar kuma tana gabanka, ka zaunar da mahaifinka da ’yan’uwanka a sashe mafi kyau na ƙasar, bari su zauna a Goshen. Idan kuma ka ga waɗansu a cikinsu da suka fi dacewa, sai ka sa su lura mini da shanuna.”7Sa’an nan Yusuf ya shigar da Yaƙub mahaifinsa, ya gabatar da shi a gaban Fir’auna. Bayan Yaƙub ya albarkaci Fir’auna,8sai Fir’auna ya tambaye shi, “Shekarunka nawa da haihuwa?”9Yaƙub kuwa ya ce wa Fir’auna, “Shekarun hijirata, shekaru ɗari da talatin ne. Shekaruna kaɗan ne cike da wahala, ba za a kuwa daidaita su da shekarun hijirar kakannina ba.”10Sai Yaƙub ya albarkaci Fir’auna, ya yi masa bankwana, sa’an nan ya fita.11Ta haka Yusuf ya zaunar da mahaifinsa da ’yan’uwansa a Masar, ya ba su mallaka a sashe mafi kyau na ƙasar, a yankin nan na Rameses, kamar yadda Fir’auna ya umarta.12Yusuf ya kuma tanada wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa da dukan gidan mahaifinsa, abinci bisa ga yawan ’ya’yansu.13A yanzu, a cikin ƙasar duka, ba abinci, gama yunwa ta yi tsanani ƙwarai, har ƙasar Masar da ƙasar Kan’ana suka shiga matsananciyar wahala!14Yusuf ya tattara dukan kuɗaɗen da suke a Masar da Kan’ana don biyan hatsin da suke saya, ya kuwa kawo su a fadan Fir’auna.15Sa’ad da kuɗin mutanen Masar da Kan’ana suka ƙare, dukan Masar ta zo wurin Yusuf ta ce, “Ka ba mu abinci. Me zai sa mu mutu a idanunka? Kuɗinmu duk sun ƙare.”16Yusuf ya ce, “To, ku kawo dabbobinku, zan sayar muku da abinci a madadin dabbobinku, tun da kuɗinku ya ƙare.”17Saboda haka suka kawo dabbobinsu wa Yusuf, ya kuma ba su abinci a madadin dawakai, tumaki da awaki, shanu da jakunansu. Ya kuwa ba su abinci a madadin dabbobinsu, a wannan shekara.18Sa’ad da wannan shekara ta ƙare, sai suka zo wurinsa a shekara ta biye suka ce, “Ba za mu ɓoye maka ba ranka yă daɗe, kuɗinmu sun ƙare, dabbobinmu kuma sun zama naka. Ranka yă daɗe, in ban da jikunanmu da gonakinmu, ba abin da ya rage mana.19Kada ka bar mu mu mutu, ka yi wata dabara! Kada ka bari mu rasa gonakinmu. Ka musaye mu da abinci, mu da gonakinmu. Mu kuwa za mu zama bayin Fir’auna. Ka ba mu iri don mu rayu, kada mu mutu, don kuma kada gonakin ƙasarmu su zama kango.”20Ta haka Yusuf ya saya wa Fir’auna ƙasar Masar duka, gama Masarawa duka sun sayar da gonakinsu, saboda yunwa ta tsananta musu. Ƙasar ta zama mallakar Fir’auna.21Yusuf kuwa ya mai da mutanen bayi, daga wannan iyakar Masar zuwa wancan.22Amma bai sayi gonakin firistoci ba, gama suna karɓa rabo daga Fir’auna ne, suna kuma da isashen abinci daga rabon da Fir’auna yake ba su. Dalilin ke nan da ba su sayar da gonakinsu ba.23Yusuf ya ce wa mutane, “Yanzu da na saye ku da kuma gonakinku a yau wa Fir’auna, ga iri don ku shuka a gonaki.24Amma sa’ad da hatsi suka nuna, za ku ba da kashi ɗaya bisa biyar ga Fir’auna. Sauran kashi huɗu bisa biyar kuma ku riƙe a matsayin iri don gonaki da kuma abinci wa kanku da gidajenku da kuma ’ya’yanku.”25Suka ce, “Ka ceci rayukanmu, in ya gamshe ka, ranka yă daɗe, za mu zama bayin Fir’auna.”26Ta haka Yusuf ya kafa wannan ya zama doka game da ƙasa a Masar, har yă zuwa yau cewa kashi ɗaya bisa biyar na amfani gona ya zama na Fir’auna. Gonakin firistoci ne kaɗai ba su zama na Fir’auna ba.27To, Isra’ilawa suka zauna a Masar a yankin Goshen. Suka mallaki filaye a can, suka riɓaɓɓanya suka ƙaru ƙwarai.28Yaƙub ya yi zama a Masar shekaru goma sha bakwai, yawan shekarunsa duka sun zama ɗari da arba’in da bakwai.29Sa’ad da lokaci ya gabato da Isra’ila zai mutu, sai ya kira ɗansa Yusuf, ya ce masa, “Ka yi mini wannan alheri, ka sa hannunka ƙarƙashin cinyar ƙafata, ka yi mini alkawari saboda ina roƙonka kaɗa ka bizne ni a Masar,30amma sa’ad da na huta da kakannina, ka ɗauke ni, ka fid da ni daga Masar, ka binne ni a inda aka binne su.” Yusuf ya ce, “Zan yi yadda ka faɗa.”31Yaƙub ya ce, “Ka rantse mini.” Sai Yusuf ya rantse masa, Isra’ila kuwa ya yi godiya ga Allah yayinda ya jingina a kan sandansa.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Sabon Rai Don Kowa 2020 Farawa 47 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/genesis/047.mp3 50 47