× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 Farawa FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 48 12345678910111213141516171819202122232425262728293031323334353637383940414243444546474849501 1 1 : 1 123456789101112131415161718192021221 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Farawa 48 Adana Bayanan kula 1Bayan wani lokaci aka faɗa wa Yusuf, “Mahaifinka yana ciwo.” Sai ya ɗauki ’ya’yansa maza biyu, Manasse da Efraim suka tafi tare da shi.2Sa’ad da aka faɗa wa Yaƙub, “Ɗanka Yusuf ya zo gare ka,” sai Isra’ila ya ƙoƙarta ya tashi ya zauna a kan gado.3Yaƙub ya ce wa Yusuf, “Allah Maɗaukaki ya bayyana gare ni a Luz a ƙasar Kan’ana, a can ya albarkace ni4ya kuma ce mini, ‘Zan sa ka yi ta haihuwa ka kuma riɓaɓɓanya, za ka ƙaru a yawa. Zan mai da kai al’ummar mutane, zan kuma ba ka wannan ƙasa tă zama madawwamiyar mallaka ga zuriyarka a bayanka.’5“To, yanzu, ’ya’ya mazanka biyu da aka haifa maka a Masar kafin in zo a nan za su zama nawa; Efraim da Manasse za su zama nawa, kamar yadda Ruben da Simeyon suke nawa.6Duk waɗansu ’ya’yan da aka haifa maka bayansu za su zama naka; a yankin da suka gāda za a lissafa a ƙarƙashin sunayen ’yan’uwansu.7Yayinda nake dawowa daga Faddan Aram, cikin baƙin cikina Rahila ta rasu a ƙasar Kan’ana yayinda muke kan hanya, ’yar rata daga Efrata. Saboda haka na binne ta a can kusa da hanya zuwa Efrata” (wato, Betlehem).8Sa’ad da Isra’ila ya ga ’ya’yan Yusuf maza, sai ya yi tambaya, “Su wane ne waɗannan?”9Yusuf ya ce wa mahaifinsa, “Su ne ’ya’yan da Allah ya ba ni a nan.” Sa’an nan Isra’ila ya ce, “Kawo mini su saboda in albarkace su.”10Yanzu fa idanun Isra’ila sun fara rasa ƙarfi saboda tsufa, har ba ya iya gani sosai. Saboda haka Yusuf ya kawo ’ya’yansa maza kusa da shi, sai mahaifinsa ya sumbace su ya rungume su.11Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ban yi tsammani zan ga fuskarka kuma ba, yanzu kuwa Allah ya bar ni in ga ’ya’yanka su ma.”12Sa’an nan Yusuf ya ɗauke su daga gwiwoyin Isra’ila ya rusuna da fuskarsa har ƙasa.13Yusuf ya ɗauke su biyu, Efraim a damansa zuwa hagun Isra’ila, Manasse kuma a hagunsa zuwa hannun daman Isra’ila, ya kuma kawo su kusa da shi.14Amma Isra’ila ya miƙa hannun damansa ya sa shi a kan Efraim, ko da yake shi ne ƙaramin, ta wurin harɗewa hannuwansa, ya sa hannun hagunsa a kan Manasse, ko da yake Manasse ne ɗan farinsa.15Sa’an nan ya albarkaci Yusuf ya ce, “Bari Allah a gaban wanda kakannina Ibrahim da Ishaku suka yi tafiya, Allahn da ya zama makiyayina dukan raina zuwa wannan rana,16Mala’ikan da ya cece ni daga dukan cuta bari yă albarkaci samarin nan. Bari a kira su da sunana da sunayen kakannina Ibrahim da Ishaku bari kuma su ƙaru ƙwarai a bisa duniya.”17Sa’ad da Yusuf ya ga mahaifinsa yana sa hannun damansa a kan Efraim bai ji daɗi ba; saboda haka ya ɗauke hannun mahaifinsa ya cire shi daga kan Efraim zuwa kan Manasse.18Yusuf ya ce masa, “A’a, mahaifina, wannan shi ne ɗan farin; ka sa hannunka na dama a kansa.”19Amma mahaifinsa ya ƙi ya ce, “Na sani, ɗana, na sani. Shi ma zai zama mutane, zai kuma zama mai girma. Duk da haka ɗan’uwansa zai zama mai girma fiye da shi, kuma zuriyarsa za tă zama ƙungiyar al’ummai.”20Ya albarkace su a wannan rana ya ce, “A cikin sunanku Isra’ila zai sa wannan albarka ‘Bari Allah yă sa ku zama kamar Efraim da Manasse.’ ” Saboda haka ya sa Efraim gaban Manasse.21Sa’an nan Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Ina gab da mutuwa, amma Allah zai kasance tare da ku22Kuma gare ka, a matsayi wanda yake kan ’yan’uwanka, na ba da gonar da na karɓe daga Amoriyawa da takobi da kuma bakana.”Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Sabon Rai Don Kowa 2020 Farawa 48 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/genesis/048.mp3 50 48