× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Madurese Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 Mattiyu FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 15 123456789101112131415161718192021222324252627281 1 1 : 21 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132333435363738391 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Mattiyu 15 Adana Bayanan kula 1Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka zo wurin Yesu daga Urushalima suka yi tambaya suka ce,2“Me ya sa almajiranka suke karya al’adun dattawa? Ba sa wanke hannuwansu kafin su ci abinci!”3Yesu ya amsa ya ce, “Ku ma me ya sa kuke karya dokar Allah saboda al’adarku?4Gama Allah ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, kuma duk wanda ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa dole a kashe shi.’5Amma ku kukan ce, in wani ya ce wa mahaifinsa ko mahaifiyarsa, ‘Duk taimakon da dā ya kamata za ku samu daga gare ni an ba wa Allah,’6ba zai ‘girmama mahaifinsa’ da shi ba. Ta haka kun yi banza da maganar Allah saboda al’adarku.7Ku munafukai! Daidai ne Ishaya ya yi annabci a kanku da ya ce,8“ ‘Waɗannan mutane da baki kawai suke girmama ni, amma zukatansu suna nesa da ni.9A banza suke mini sujada, koyarwarsu, dokoki ne kawai da mutane suke koyarwa.’ ”10Sai Yesu ya kira taron wurinsa ya ce, “Ku saurara ku kuma gane.11Abin da yake shiga bakin mutum ba ya ƙazantar da shi, sai dai abin da yake fitowa daga bakinsa, shi ne yake ƙazantar da shi.”12Sai almajiran suka zo wurinsa suka ce, “Ka san cewa Farisiyawa ba su ji daɗi sa’ad da suka ji wannan ba?”13Ya amsa ya ce, “Duk tsiron da Ubana na sama bai shuka ba, za a tumɓuke shi daga saiwoyi.14Ku ƙyale su, ai, makafin jagorai ne. In makaho ya yi wa makaho jagora, dukansu za su fāɗa a rami.”15Bitrus ya ce, “Ka bayyana mana wannan misali.”16Yesu ya tambaye su ya ce, “Har yanzu ba ku gane ba ne?17Ba ku gane cewa duk abin da ya shiga baki yakan wuce ciki ne daga nan kuma yă fita daga jiki ba?18Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum.19Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa.20Waɗannan su ne suke ƙazantar da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannuwa ba, ba ya ƙazantar da mutum.”21Barin wurin ke nan, sai Yesu ya janye zuwa yankin Taya da Sidon.22Wata mutuniyar Kan’ana daga wajajen ta zo wurinsa, tana ihu tana cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai! ’Yata tana shan wahala ƙwarai daga aljanin da yake cikinta.”23Yesu bai ce mata uffam ba. Saboda haka almajiransa suka zo wurinsa suka roƙe shi suka ce, “Ka kore ta tă tafi, tana ta binmu tana damunmu da ihu.”24Ya amsa ya ce, “An aiko ni wurin ɓatattun tumakin Isra’ila ne kaɗai.”25Sai macen ta zo ta durƙusa a gabansa ta ce, “Ubangiji, ka taimake ni!”26Ya amsa ya ce, “Ba daidai ba ne a ɗauki abincin yara a jefa wa karnukansu.”27Ta amsa, ta ce, “I, Ubangiji, amma karnuka ma sukan ci gutsattsarin da sukan fāɗi daga teburin maigidansu.”28Sa’an nan Yesu ya amsa ya ce, “Mace, kina da bangaskiya mai yawa! An biya miki bukatarki.” ’Yarta kuwa ta warke nan take.29Yesu ya tashi daga nan ya bi ta gefen Tekun Galili. Sa’an nan ya haura gefen wani dutse ya zauna.30Taron mutane mai girma kuwa suka zo wurinsa, suna kawo masa guragu, makafi, shanyayyu, kurame da dai waɗansu da yawa, suka kuwa kwantar da su a gabansa; ya kuma warkar da su.31Mutanen kuwa suka yi mamaki sa’ad da suka ga kurame suna magana, shanyayyu suna samun lafiya, guragu suna takawa, makafi kuma suna ganin gari. Sai suka yabi Allah na Isra’ila.32Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Ina jin tausayin mutanen nan; gama kwana uku ke nan suke tare da ni ba abin da za su ci. Ba na so in sallame su da yunwa, don kada su kāsa a hanya.”33Sai almajiransa suka amsa suka ce, “Ina za mu sami isashen burodi a wannan wurin da babu kowa mu ciyar da irin taron nan?”34Yesu ya tambaye su, “Burodi guda nawa kuke da shi?” Suka amsa suka ce, “Guda bakwai da ’yan ƙananan kifaye.”35Ya sa taron su zazzauna a ƙasa.36Sa’an nan ya ɗauki burodi guda bakwai da kuma kifayen nan, da ya yi godiya, sai ya kakkarya su ya ba wa almajiran, su kuma suka ba wa mutane.37Duk kuwa suka ci, suka ƙoshi. Daga baya almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna bakwai.38Yawan waɗanda suka ci kuwa, maza dubu huɗu ne, ban da mata da yara.39Bayan Yesu ya sallami taron, sai ya shiga jirgin ruwa ya tafi wajajen Magadan.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Sabon Rai Don Kowa 2020 Mattiyu 15 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/matthew/015.mp3 28 15