× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Irmiya FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 11 123456789101112131415161718192021222324252627282930313233343536373839404142434445464748495051521 1 1 : 1 12345678910111213141516171819202122231 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Irmiya 11 Adana Bayanan kula 1Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji.2“Ka saurari zancen wannan alkawari ka kuma faɗe su ga mutanen Yahuda da kuma waɗanda suke zaune a Urushalima.3Ka faɗa musu cewa ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa, ‘La’ananne ne wanda bai kula da zancen alkawarin nan ba,4zancen da na umarci kakanni-kakanninku sa’ad da na fitar da su daga Masar, daga cikin tanderun narkewar ƙarfe.’ Na ce, ‘Ku yi mini biyayya ku kuma aikata kowane abin da na umarce ku, za ku kuwa zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnku.5Sa’an nan zan cika rantsuwar da na yi wa kakanni-kakanninku, da zan ba su ƙasa mai zub da madara da kuma zuma’ ƙasar da kuka mallaka a yau.” Sai na amsa na ce, “Amin, Ubangiji.”6Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuda da titunan Urushalima duka cewa, ‘Su saurari zancen alkawarin nan, su aikata.7Daga lokacin da na fitar da kakanni-kakanninku daga Masar har yă zuwa yau, na gargaɗe su sau da sau, ina cewa, “Ku yi mini biyayya.”8Amma ba su kasa kunne ko su saurara ba, a maimako, sai suka bi taurinkai na mugayen zukatansu. Saboda haka na kawo musu dukan la’anonin alkawarin da na riga na umarce su, su bi amma ba su kiyaye ba.’ ”9Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, “Akwai maƙarƙashiya a cikin mutanen Yahuda da waɗanda suke zaune a Urushalima.10Sun koma ga zunuban kakanni kakanninsu, waɗanda suka ƙi su saurari maganata. Suka bi waɗansu alloli don su bauta musu. Da gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda duk sun take alkawarin da na yi da kakanni kakanninsu.11Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan kawo masifa a kansu wadda ba za su iya tsere mata ba. Ko da yake suna kuka gare ni, ba zan saurare su ba.12Garuruwan Yahuda da mutanen Urushalima za su tafi su yi kuka ga allolin da suke ƙona wa turare, amma ba za su taimake su ba sam sa’ad da masifar ta auku.13Kuna da alloli masu yawa yadda kuke da garuruwa, ya Yahuda; kuma bagadan da kuka yi don ƙona turare wa allahn nan Ba’al abin kunya sun yi yawa kamar titunan Urushalima.’14“Kada ka yi addu’a domin wannan mutane ko ka miƙa wani roƙo ko kuka dominsu, domin ba zan saurara ba sa’ad da suka kira gare ni a lokacin ƙuncinsu.15“Mene ne ƙaunatacciyata take yi a haikali da yake ta yin ƙulle-ƙullen mugayen makircinta tare da mutane masu yawa? Tsarkakar nama zai iya kawar da hukuncinki? Sa’ad da kike yin muguntarki sa’an nan ki yi farin ciki.”16Ubangiji ya kira ki itacen zaitun mai inuwa kyakkyawa mai ’ya’ya masu kyau. Amma da ƙugin babbar hadari zai cinna masa wuta, rassansa za su kakkarye.17Ubangiji Maɗaukaki, wanda ya dasa ki, ya furta miki masifa, domin gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda sun aikata mugunta suka kuma tsokane ni in yi fushi ta wurin ƙona wa Ba’al turare.18Domin Ubangiji ya bayyana mini maƙarƙashiyarsu, na santa, gama a wannan lokaci ya nuna mini abin da suke yi.19Na kasance kamar ɗan rago marar faɗa wanda aka kai mayanka; ban gane cewa sun ƙulla mini maƙarƙashiya, suna cewa, “Bari mu lalatar da itacen duk da ’ya’yansa; bari mu datse shi daga ƙasar masu rai, har da ba za a ƙara tunawa da sunansa ba.”20Amma, ya Ubangiji Maɗaukaki, kai da kake yin shari’a da adalci kake gwada zuciya da kuma tunani, ka sa in ga sakayyar da za ka yi musu, gama a gare ka na danƙa maganata.21“Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da mutanen Anatot, waɗanda suke neman ranka suna kuma cewa, ‘Kada ka yi annabci da sunan Ubangiji in ba haka za ka mutu a hannunmu’22saboda haka ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, ‘Zan hukunta su. Samarinsu za su mutu ta wurin takobi, ’ya’yansu maza da mata kuwa ta wurin yunwa.23Babu raguwar da za a bar musu, domin zan kawo masifa a kan mutanen Anatot a shekarar hukuncinsu.’ ”Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Irmiya 11 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/jeremiah/011.mp3 52 11