× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 2020 202020101 1 1 Karin Magana FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 28 123456789101112131415161718192021222324252627282930311 1 1 : 15 123456789101112131415161718192021222324252627281 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Karin Magana 28 Adana Bayanan kula 1Mugu yakan gudu ko babu wanda yake korarsa, amma adalai suna da ƙarfin hali kamar zaki.2Sa’ad da ƙasa ta yi tayarwa, takan kasance da masu mulki da yawa, amma mai fahimi da sani kan mai da zaman lafiya.3Mai mulkin da ya danne talakawa yana kama da ruwan saman da ya lalatar da hatsi.4Duk waɗanda ba sa bin doka yabon mugaye suke yi, amma waɗanda suke yin biyayya da doka suna gāba da mugaye ke nan.5Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke neman Ubangiji sun santa sosai.6Gara matalauci wanda yake tafiya babu abin zargi da mai arziki wanda hanyoyinsa mugaye ne.7Duk wanda ya kiyaye doka ɗa ne mai la’akari, amma wanda yake abokantaka da masu zari yakan jawo wa mahaifinsa kunya.8Duk wanda ya tara dukiyarsa ta wurin ba da bashi da ruwan da ya wuce misali yana tara wa wani ne wanda zai yi wa talakawa alheri.9In wani ya yi kunnuwa ƙashi ga doka ko addu’arsa ma abar ƙyama ce.10Duk wanda ya jagorance masu aikata gaskiya a hanyar mugunta zai fāɗa cikin tarkonsa amma marasa abin zargi za su sami gādo mai kyau.11Mai arziki zai yi zato shi mai hikima ne a ganinsa, amma matalauci mai basira ya fi shi sanin abin da yake daidai.12Sa’ad da adalai suka yi nasara, kowa yakan yi biki; amma sa’ad da mugu ya samu shugabanci, mutane sukan yi ta ɓuya.13Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara, amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.14Mai albarka ne mutumin da kullum yake jin tsoron Allah, amma duk wanda ya taurare zuciyarsa yakan shiga wahala.15Kamar rurin zaki ko sanɗar beyar haka mugun mutum mai mulki a kan mutane marasa ƙarfi yake.16Mugu mai mulki ba shi da azanci, amma duk wanda yake ƙin ƙazamar riba yakan yi tsawon rai.17Mutumin da laifin kisa ya yi ta damunsa zai zama mai gudu don tsoro har mutuwa; kada wani ya taimake shi.18Duk wanda ya yi tafiya marar abin zargi zai zauna lafiya, amma duk wanda hanyoyinsa mugaye ne zai fāɗi nan da nan.19Duk wanda ya nome gonarsa zai sami amfani a yalwace, amma duk wanda yake zaman banza zai zama matalauci a koyaushe.20Mutum mai aminci zai cika da albarka, amma duk mai son yin arziki dare ɗaya zai sha hukunci.21Nuna sonkai ba shi da kyau, duk da haka mutum zai aikata abin da ba daidai ba saboda ’yar ƙaramar rashawa.22Mai rowa yana alla-alla ya yi arziki bai san cewa talauci ne ke jiransa ba.23Duk wanda ya tsawata wa wani mutum zai sami yabo a ƙarshe fiye da wanda yake mai daɗin baki.24Duk wanda ya yi wa mahaifin ko mahaifiyarsa sata ya kuma ce, “Ai, ba laifi ba ne” abokin mai hallakarwa ne shi.25Mai haɗama yakan jawo tā-da-na-zaune-tsaye, amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai yi nasara.26Duk mai dogara ga kansa wawa ne, amma duk wanda yake tafiya da hikima zai zauna lafiya.27Duk wanda yake bayarwa ga matalauta ba zai rasa kome ba, amma duk wanda bai kula da su ba yana samu la’ana masu yawa.28Sa’ad da mugu ya samu shugabanci, mutane sukan yi ta ɓuya; amma sa’ad da mugu ya hallaka, adali kan ci gaba cikin arziki da lafiya.Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Used with permission. All rights reserved worldwide. Sabon Rai Don Kowa 2020 Karin Magana 28 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/proverbs/028.mp3 31 28