× Harshe Turai Rashanci Belarusiyanci Yukreniyanci Yaren mutanen Poland Sabiyanci Bulgaria Slovakiyan Czech Romaniyanci Moldoviyanci Azerbaijan Armeniyanci Jojiyanci Albaniyanci Avar Bashkir Tatar Checheniya Slobaniyanci Kuroshiya Estoniyanci Latvia Lituweniyanci Harshen Hungary Yaren mutanen Finland Yaren mutanen Norway Yaren mutanen Sweden Icelandic Girkanci Macedonia Bajamushe Bavarian Yaren mutanen Holland Danish Welsh Gaelic Irish Faransanci Basque Katalaniyanci Italiyanci Galacian Romani Bosnian Kabardian Amirka ta Arewa Turanci Kudancin Amurka Sifeniyanci Fotigal Guarani Quechuan Aymara Amurka ta Tsakiya Jamaica Nahuatl Kiche Qeqchi Haiti Gabashin Asiya Sinanci Jafananci Yaren Koriya Mongoliyanci Uyghur Hmong Tibetian Kudu maso gabashin Asiya Malesiya Burma Chin Nepali Cebuano Tagalog Kambodiyanci Thai Indonesiyanci Sundanese Vietnam Javanisanci Lao Iban IuMien Kachin Lahu Aceh Balinese Bugis Pampanga Sasak Shan Waray Kudancin Asiya Hindi Оdia Awadhi Mizo Kannada Malayalam Marathi Gujarati Tamil Telugu Harshen Punjabi Kurukh Assamese Maithili Bengali Urdu Sinhala Dogri Haryanvi Meitei Konkani Santali Sindhi Koya Thado Sanskrit Devanagari Adilabad Gondi Ahirani Balochi Bundeli Chhattisgarhi Garhwali Kangri Kumaoni Mewari Munda Sadri Seraiki Shekhawati Sylheti Bagri Bhilali Bodo Braj Tulu Asiya ta Tsakiya Kirgiziya Uzbek Tajik Turkmen Kazakhstan Karakalpak Gabas ta Tsakiya Baturke Ibrananci Larabci Farisanci Kurdawa Mazanderani Pashto 'Yan Koftik Afirka Afirkaans Xhosa Zulu Ndebele Sotho Amharic Wolaytta Dan Najeriya Mossi Ika Dinka Kabyle Ewe Swahili Maroko Somalian Shona Madagaska Igbo Lingala Baoule Siswati Tsonga Tswana Gambiya Yarbawa Kamba Kinyarwanda Hausa Chewa Luo Makua Dyula Fulfulde Kalenjin Kikuyu Kikwango Kirundi Krio Nigerian Pidgin Oromo Tshiluba Tshivenda Twi Umbundu Lugbara Luguru Pular Gussi Maasai Turkana Moba Nuer Shilluk Tamasheq Makonde Bemba Fon Hadiyya Ibibio Kimbundu Kimiiru Lango Liberian Kreyol Lomwe Mende Morisyen Ndau Nyankole Sena Sidamo Soga Songe Sukuma Tarifit Teso Tiv Zande Dagbani Edo Kituba Nahiyar Australiya New Zealand Papua New Guinea Tsoffin Harsuna Aramaic Latin Esperanto 1 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Sabon Rai Don Kowa 2020أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا 2020Littafi Mai Tsarki 19791 1 1 Firistoci FarawaFitowaFiristociƘidayaMaimaitawar ShariʼaYoshuwaMahukuntaRut1 Samaʼila2 Samaʼila1 Sarakuna2 Sarakuna1 Tarihi2 TarihiEzraNehemiyaEstaAyubaZaburaKarin MaganaMai HadishiWaƙar WaƙoƙiIshayaIrmiyaMakokiEzekiyelDaniyelHosiyaYowelAmosObadiyaYunanaMikaNahumHabakkukZefaniyaHaggaiZakariyaMalaki--- --- ---MattiyuMarkusLukaYohannaAyyukan ManzanniRomawa1 Korintiyawa2 KorintiyawaGalatiyawaAfisawaFilibbiyawaKolossiyawa1 Tessalonikawa2 Tessalonikawa1 Timoti2 TimotiTitusFilemonIbraniyawaYaƙub1 Bitrus2 Bitrus1 Yohanna2 Yohanna3 YohannaYahudaRuʼuya ta Yohanna1 1 1 22 1234567891011121314151617181920212223242526271 1 1 : 1 1234567891011121314151617181920212223242526272829303132331 1 1 Sabon Rai Don Kowa 2020 Firistoci 22 Adana Bayanan kula 1Ubangiji ya ce wa Musa,2“Faɗa wa Haruna da ’ya’yansa maza, su lura da tsarkakakkun abubuwan da Isra’ilawa suka keɓe gare ni da bangirma, saboda ba za su ƙazantar da sunana mai tsarki ba. Ni ne Ubangiji.3“Faɗa musu cewa, ‘Don tsararraki masu zuwa, in wani zuriyarku ya ƙazantu, duk da haka ya kusaci tsarkakakku hadayun da Isra’ilawa suka keɓe ga Ubangiji, dole a raba wannan mutum daga gabana. Ni ne Ubangiji.4“ ‘In zuriyar Haruna yana da kuturu, ko mai ɗiga, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwa ba, sai lokacin da ya tsarkaka. Duk wanda ya taɓa wani abu marar tsarki na mamaci, ko wanda maniyyinsa yake ɗiga,5da duk kuma wanda ya taɓa wani abu mai rarrafe wanda yake ƙazantarwa, ko kuwa wani mutum mai ƙazanta,6duk mutumin da ya taɓa kowane irin abu haka, zai ƙazantu har yamma, ba kuwa zai ci daga cikin tsarkakakkun abubuwan nan ba, sai ya yi wanka tukuna.7Sa’ad da rana ta fāɗi, zai zama tsarkakakke, bayan wannan kuwa zai iya cin tsarkakakkun hadayu, gama abincinsa ne.8Kada yă ci wani abin da ya mutu mushe, ko wanda namun jeji suka yayyaga, don kada yă ƙazantar da kansa. Ni ne Ubangiji.9“ ‘Firistoci za su kiyaye umarnaina don kada su yi laifi su mutu saboda sun rena su. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da su masu tsarki.10“ ‘Duk wanda ba daga cikin iyalin firistoci ba, ko da yake yana zama tare da su, ko kuwa an ɗauke shi yana yin musu aiki, ba zai ci daga cikin tsarkakakkun hadayun ba.11Amma in firist ya sayi bawa da kuɗi, ko kuwa in an haifi bawan a gidansa, wannan bawan zai iya cin tsattsarkan abincin.12In ’yar firist ta auri wani da ba firist ba, ba za tă ci wani tsarkakakkun sadaka ba.13Amma idan ’yar firist ta zama gwauruwa ko sakakkiya, ba ta da ’ya’ya, ta kuwa dawo don tă zauna a gidan mahaifinta kamar matashiya, za tă iya cin abincin.14“ ‘In wani ya ci tsarkakakken abinci cikin kuskure, dole yă maido wa firist hadayar, yă kuma ƙara kashi ɗaya bisa biyar na tamanin abin.15Firist ɗin ba zai ƙasƙantar da tsarkakakkun hadayun da Isra’ilawa suka kawo ga Ubangiji16ta wurin barinsu su ci tsarkakakkun hadayu, ta yin haka su jawo wa kansu laifin da zai bukaci biya ba. Ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.’ ”17Ubangiji ya ce wa Musa,18“Yi wa Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa magana ka ce musu, ‘In waninku, ko mutumin Isra’ila, ko baƙon da yake zama a Isra’ila, ya kawo kyauta don hadaya ta ƙonawa ga Ubangiji, ko don yă cika alkawari, ko kuwa a matsayin hadaya ta yardar rai,19dole ku miƙa dabba namiji marar lahani, daga shanu, tumaki, ko awaki, domin yă zama yardajje a madadinku.20Kada ku kawo wani abu mai lahani, domin ba zai zama yardajje ba a madadinku.21Sa’ad da wani ya kawo hadaya ta salama daga garken shanu, ko na tumaki, ga Ubangiji don yă cika wani alkawari na musamman, ko hadaya ta yardar rai, dole yă zama marar lahani, ko tabo, don yă zama yardajje.22Kada ku miƙa wa Ubangiji dabbobi makafi, ko naƙasassu, ko masu gundumi, ko masu ɗiga, ko masu susa, ko masu kirci. Kada ku sa wani daga cikin waɗannan a bisa bagade a matsayin hadaya, gama hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.23Za ku iya miƙa hadaya ta yardar rai da maraƙi, ko tunkiya mai naƙasa, ko marar cikakken lafiya, amma ba za tă zama yardajje don cika alkawarin da aka yi ba.24Ba za ku miƙa wa Ubangiji dabbar da lunsayinta yake da ƙujewa, ko dandaƙewa, ko yagewa, ko yankewa ba.25Ba za ku kuma karɓi irin waɗannan dabbobi daga hannun baƙi ku miƙa su a matsayin abinci ga Allahnku ba. Ba za su zama yardajje a madadinku ba, domin sun naƙasa, suna kuma da lahani.’ ”26Ubangiji ya ce wa Musa,27“Sa’ad da aka haifi ɗan maraƙi, tunkiya, ko akuya, sai yă kasance da mahaifiyarsa kwana bakwai. Daga rana ta takwas zuwa gaba, zai zama yardajje hadaya, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.28Kada a yanka saniya, ko tunkiya da ɗanta rana ɗaya.29“Sa’ad da kuka miƙa hadaya ta godiya ga Ubangiji, ku miƙa ta a yadda za tă zama yardajje a madadinku.30Dole a ci hadayar a ranar; kada a bar saura sai da safe. Ni ne Ubangiji.31“Ku kiyaye dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji.32Kada ku ƙasƙantar da sunana mai tsarki. Dole Isra’ilawa su gane Ni mai tsarki ne. Ni ne Ubangiji, wanda ya keɓe ku a matsayin tsarkaka33da kuma wanda ya fitar da ku daga Masar don in zama Allahnku. Ni ne Ubangiji.”Hausa Bible 2020 Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc. An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya. Hausa Contemporary Bible™ Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc. Sabon Rai Don Kowa 2020 Firistoci 22 00:00:00 00:00:00 0.5x 2.0x https://beblia.bible:81/BibleAudio/hausa2013/leviticus/022.mp3 27 22